Dangin Uba (17 &18)



Dangin Uba


Dangin Uba



Page (17&18) 

Haisam da Maisha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?"

"Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?"

"To ai Ni bana salllama" Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me. Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?"

Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours"

Yace "Naga kunyi sauri ne ai"

Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?"

Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi"

Tace "To a dawo lafiya"

Ya amsa da "Ameen"

Sai yayi ficewar sa.

Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa. Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwabar nan Haka. Haisam yace "Daddy ai saima abinda ya karu, Mijin ta zai Sha wahala sosai don na tabbata ko da bayan ta haihuwane Reno biyu zaiyi"

A zuciyar Tace "Zaka Sha Reno dai, don kaine mijin nawa Insha Allah" a bayyane Kuma Tace " daddy kace Masa ya daina tsokana ta" har da bubbuga kafar ta kamar yarinya Yar shekara biyar daddy yace "Son ka daina tsokanar ta. Haisam dariya kawai yayi baice komai ba, mummy ce ta Shigo parlor taci kwalliya sai zuba kamshi take Tace "Daga dawowar sa kun sashi a gaba da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karba jakar sa. 

Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta"

Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa"

"Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku"

A tare sukace toh.

Karban jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa"

"Anki d'in mijinkine ko mijina?"

Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?"

Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun dazu ta wuce dakin sa. Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori. Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi"

"kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? "

"Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?"

"Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki."

Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo.

Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?"

Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko"

" Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace"

"Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo"

"nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare.

Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki"

"sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu"

"No yi hakuri nayi shiru"

Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta"

Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa"

"Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?

Bata so hakan ba Dole ce tasa ta hakura yayiwa su mummy sai da safe ya wuce part d'insu Yana tafiya Ma'isha itama tashi ta shige dakin ta. Haisam na shiga daki ya ban d'aki ya fada yayi wanka ya sanya vest da d'an gajeren wandon sa ya dale Kan gado ya bude datar sa ya Fara chatting, emoji da stickers na kuka ya Fara cin karo dasu Maisha ta jero Masa dama yasan za a Rina Nan ya shiga rarrashin ta suna cikin chat din ne bakuwar number ta kirasa.

Yana picking Tace "Haba yallabai kasa ina ta jiran ka, nan ne ma ya tuna cewar yace zai kirata dafe kansa yayi yace "Am so sorry Aysha na danyi busy ne gafar ce ni"

Murmushi tayi ko ba komai bai manta sunan ta ba, tace "Bakomai yallabai Ni da na damu da nayi magana da kai ai na kiraka"

Murmushi yayi yace "Afwan ina jinki"

"Ok dama ba wani abu bane ba, so nake Dan Allah ka Zama Tutor na"

"Tutor dai? 'dan Ni d'in Nan bani da wannan ilimin ai Ni dolo ne fa"

Yar karamar dariya tayi Tace "na amince ka koya min dolon cin naka, duk da nasan Kai ba dolon bane ba sai dai in rowa zaka min Kar na karu da kai sai na hakura. Murmushi yayi yace "To yaushe kike so mu Fara?"

Tace "Ko gobe ma"

"No gobe Sunday ba inda nake zuwa ina gida, ki dai bari idan muka hadu Monday mayi maganar"

Cikin murna Tace "Toh nagode sosai"

"Bakomai sai da safe"

Ya katse wayar Aysha bin wayan tayi da kallo tace "Mtssw ya katsewayar kamar shi ya Kirani" wurga wayan tayi akan gado ta kwanta ta fara sharar baccin ta dama ta Riga ta shirya cikin kayan baccin ta. Ma'isha kuwa ganin bai mata reply ba tayi tunanin ko bacci ne ya dauke sa, ta shiga kiransa Amma busy, ji tayi kamar ta kurma ihu, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga wanka ta d'aura da alwala,bayan ta fito tayi shafa'i da wutiri bayan ta idar ta shiga rokon Allah da ya yaye Mata sayayyar da take Masa in shi d'in ba alhairi bane a gareta ba, in ko alhairi ne yasa ya Sota kamar yadda take son.

Wayar Tace ta fara ringing tana dubawa taga yayana Yar karamar tsaki tayi Tace "wato ya gama waya da ita"

Sai da ya kusa yankewa ta sa hannu ta d'aga ta Kara a kunnen ta, yace "Haba princess kin shanyani bacci Kika yine?"

"a'a wanka na shigane"

"Shine baki fad'a min ba?"

"gani nayi kana wayar da tafini muhimmanci"

" Ki daina fad'in haka princess waya nake da wata course mate d'ina"

"Oh mace ce ma ko?"

Yace "yes"

"Na sani ai"

"Me Kika sani?"

"Babu komai"

" To hau online din mu cigaba da hirar mu"

Tace "Nikam bacci zanyi kaina ke ciwo"

Babu yanda baiyi ba ta hau Amma taki hakan yasa ya kyale ta,katse wayar yayi, yayi wurgi da ita Yana tsaki yace "Yau na kasa gane Kan yarinyar Nan ko me ya same ta oho"

Da wannan tunanin bacci yayi awun gaba da shi. Ma'isha kuwa kasa bacci tayi, tana kuncewa sa sakawa idan har bata mallaki Haisam a matsayin miji ba zata iya samun matsala, Kila ma ta rasa rayuwar ta a dalilin hakan, Amma meyasa haryanzu bai nuna Yana sonta ba. A bayyane Tace "Ya Allah kasa Yayana Yana Jin abinda Nima nake ji akan sa, Allah yasa ba Ni kadai nake haukataba" a Haka har bacci ya d'auke ta.

WASHE GARI

Ma'isha tunda tayi sallar asuba ta koma bacci bata tashi ba har sai da aka Fara Kiran sallar azahar, tana farkawa wayarta ta fara dubawa taga missed calssy da dama, amma na haisam yafi yawa harda texts shi a tunanin sa fushi ta Kuma yi dashi. Murmushi kawai tayi ta tura Masa text am sorry Yaya na bacci nake , wayar na silent ne shiyasa banji ba. 

Yana gani ya Mata reply da *"okay idan kin shirya ki Sanar dani Ina d'akina sai na kai ki saloon din. 

Ta amsa reply da Alright

tashi tashiga wanka,sai da tayi sallar azahar kana tashirya cikin wasu lallausar riga da siket na voyel less dark blue wanda aka mata ɗinkin tamkar ajikinta aka dinka yayinda adon jikin kayan pink ta yafa pink din mayafi da takalminta hill da kuma handbag ɗinta pink yar karama ,ta saka wayarta aciki, Batayi wani kwalliya ba abisa dabi'arta na rashin damuwa da ɓata fuskar ta wajan ciki masa hayaniyar kwalliya ,Ta fesa turaren ta mai kamshi ta fito.

Tana fitowa ta samu mummy da Umma a parlor suna Hira sannan suna Kallo sama sama Umma tace " masha Allah daughter kinyi kyau" Ma'isha kanta akasa tana murmushi tace

"Nagode umma "

Mummy Tace "Yau sai ina Haka?"

"Saloon zani"

"uhmnn" kawai Tace

Tace "Sai mun dawo"

Mummy kallon ta kawai tayi Umma Tace "A dawo lafiya,Allah ya tsare"

Ta amsa da Ameen, part d'insu Haisam ta shiga Kai tsaye dakin sa ta nufa, ta tarar ya gama Shima hakan yasa basu, bata lokaci ba fita sukayi atare, sadaddiyar mota suka shiga da Alama sabuwace an wanke ta sai sheki take. Bayan sun shiga motar ya kalleta ta yace "Princess irin wannan kyawu Haka, kamar Zaki je gasar sarauniyar kyau"

Turo baki tayi cikin Shagwab'a tace "Sai yanzu ka ganni?"

Dafe Kai yayi yace "kefa na lura Sam bana Miki gwanin ta ko?"

"Ni dai bance ba, ai tun Shiga na dakin yakamata kace nayi kyau. 

"kyau din naki ne yayi yawa baki ga sai kallon ki nake ba na kasa magana,Kuma nayi maganar baki ji bane, yanzun ma dakyar maganar ta fito"

Dariya kawai tayi tana Jin dalilin kalaman sa masu sanyaya zuciya, shiyasa Bata gajiya da magana dashi bataki ace tana tare dashi ba a ko wani lokaci ba. Sunyi tafiya kusan na minti uku sai Tace "kaima fa kayi kyau sosai Yaya"

"Au ramawa zakiyi? Sai yanzu Kika ganni Kennan. 

"A a na Isa ramuwa Kuma, tun d'azu nake son fad'a maka cewar kayi kyau sosai Amma ya kasa fita yanzun ma dakyar sai da na dage na furta"

Dariya ya Shiga yi, itama tana dariya tuki yake a hankali har suka Isa saloon ta fita shi Kuma ya zauna a mota Yana jiran ta.

Fitar ta ke da wuya wayar sa ta Fara ringing Yana dubawa yaga Aysha, picking yayi bayan sun gaisa ta Fara Jan shi da Hira har ta a ka Gama wanken Kan nata suna waya da Aysha bude

motar tayi ta zauna, yace "Aisha am sorry please zan kira ki anjima"

Tace "Tohm bye" ya katse wayar.

yace "Princess har kin Gama?"

" yau Kuma Yaya? "

"Yau Kuma me? "

"To ai ka Saba cewa na dad'e ne,yau Kuma nayi sauri ko?"

Dariya yayi yace "Wallahi Aysha ce ta ke ta bani dariya"

"Wace ce Aysha Kuma?"

"course mate d'inace"

" Wato da ita yake waya Kennan jiyan ma koma wacece ke baki Isa ki rabani da Yayana ba,baki Isa ki rusa min ginin da na dad'e ina ginawa ba" take ayyanawa a ranta.

Tafi yayi Tace "Na'am"

"Lafiyan ki kuwa tunanin me kike haka?"

"Bakomai bacci nake ji yaya"

"Shopping din fa?"

" Na fasa mu koma gida kawai"

"Ikon Allah yau wa

zai Mutu princess ce tace Bata son shopping"

Kirkirerren Murmushi tayi yace " Your wish is my command"

Ya tada motar suka bar gun.

Suna Isa gida bata tsaya jiran sa ba ta bud'e motar ta fita, tarar da su Mummy ta musu sannu ta shige d'akin ta.

Umma Tace "mutanen ki sun fara"

Mummy Tace "Chan ta matse mu Basu da damuwa ne ko kadan"




Post a Comment

Previous Post Next Post