Dangin Uba (1 to 6)



Dangin Uba


DANGIN UBA



Page 1&2

Haisam shine kad'ai d'a a gun Mahaifiyar sa Wacce ta kasance talaka, Mahaifin sa ya rasu tun Haisam na 'dan shekara biyu duniya.Mahaifin sa mai kud'i ne sosai shiyasa wasu daga cikin yan uwan sa suke bakin Ciki. Duk da ya kasance Mai taimakon mutane sosai ga duk Wanda yake neman taimako daga gareshi, hakan bai Hana Yan uwansa Shirin kashe shi ba sabida su mallaki dukiyar sa.

Da sun so shi sabida shine kadai Wanda Allah Albarka ce shi da d'a na miji. A Haka, wani daga cikin su ya sa mishi guba a abinci. Mahaifin Haisam yayi duk abinda yaga zai iya don ya ceci ransa daga guban Amma ya Riga ya Masa illa a jikin sa. Bayan rashin lafiya na watanni biyu sai ya rasu, Amma Kan ya rasu ya bawa matar sa wasiya akan ta tabbar ta ilmantar da Haisam Boko da addini komin tsadan sa.

Bayan wata d'aya da rasuwar sa, wannan d'an uwan sa da yasa Masa guba yazo ya kwace dukkanin dukiyar, ya bar su ba ko sisin da za su rike. Rayuwa duk ta lalace wa Haisam da mahaifiyar sa, da kyar suke samun abinda zasu sa a cikin su, Amma duk da wahalan da suke Sha Bai Hana ta sa shi a makaranta Mai kyau ba, sabida shine wasiyar Mahaifin sa.

Haisam yaro ne Mai kokari a makaranta, ya kasance shine yake zuwa na d'aya a cikin shekaru uku da yayi a junior secondary School, tunda da ga Nan ya kafa record. Ya cigaba da kokarin da ya Saba har ya Shiga senior secondary School. A yanzu Yana aji SS3 babban matsalar sa shine inda zai sami kud'in registration na W. A. E. C.

MAKARANTA

A ko da yaushe Haisam na Zama shi kadai, baya kula kowa harkan gaban sa kawaii yake yi sannan bashi da abokai, Duk da ya kasance Yan ajinsu sukan Zo gun sa don ya ganar dasu darasussukan da ya shige musu duhu ko basu gane ba, Yana da kirki sosai ga ilimi sannnan a shirye yake da ya ga ya taimaka musu, wata Rana a aji, darasin English ake musu, Haisam na zaune kusa da Ma Isha wacce ta kasance sabuwar zuwa ce a makarantar tasu, Ma'isha yarinyar kirkice daga gidan masu kudi, Bai dad'e da aka zabi Mahaifin ta a matsayin chariman na karamar hukumar su ba.

A Lokacin da ake darasi malamar su Tace "Who can define phrase?" Duk Wanda suka amsa ba dai dai ba aka sa su kneel down. Haisam ya San amsan Kuma ya lura da Ma'isha na tsoro sabida bata San amsar ba, yayi saurin rubuta amsar a paper ya Mika mata. Nan take Ma'isha ta karb'a, malamar ta juyo gareta Tace "Ma'isha Mus'ab Aminu, answer the question, what is a phrase?"

Ma'isha mikewa tayi ta tsotsa keyan ta wasu daga cikin Yan ajin suka shiga yi mata dariya a ganin su baza ta iya bada amsar Amsar ba "A phrase is a group of words that does not contain a finite verb and cannot stand alone to make a complete sentence" ta bada amsar cikin hikima da basira, malamar Tace " Excellent, class give her a round of applause." bayan sun fita break cikin sauri ta sayi biscuits da soft drink wa Haisam.

"LHi Haisam, I want to thank you for your kind heartedness. You really saved me from the teacher's punishment and embarrassment." Ma'isha ke Wannan maganar.

"You are welcome"kawai yace mata "Please take this snacks for my appreciation" Murmushi yayi yace "No thanks, no need for these really" Cikin murya kamar zatayi kuka Tace "But please am trying to show my appreciation, Dan Allah ka karb'a" "Na sani I don't think I need it, ko da yake ban ga dalili da zaisa ki dami Kanki ba"

"Ban damu ba, ni dai Dan Allah ka karb'a Dan Allah, idan baka karb'a ba bazanji dad'i ba".

Musaddiq, da tun dazu yake kallon su ya matso kusa yace "He does not want it, is it by force? Ko da yake, ni ina bukata bari na taimaka masa. " Haisam da Ma'isha hararar sa sukayi Rai a 'bace, ganin hakan yasa yayi saurin barin wajen, Haisam karb'a yayi sannan ya mata godiya, Ma'isha ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.

"Na sani dama ka na jin yunwa, but you're just pretending" ta yi maganar a sigar tsokana. Yace " Kul, ki iya bakin ki",hakan yasa ta bar zancen.

Haisam na ci suna Hira suka gabatar da Kan su wa juna ba dad'e wa aka tashe su, wasu iyaye na zuwa d'aukan 'ya 'yan su, Driver a ka turo ya Zo d'aukan Ma'isha, Haisam na daga cikin yaran da, da kafa suke zuwa makaranta sannan su Koma da kafa, A Lokacin da Ma'isha ta ganshi ta umurci driver da ya tsaya Tace "Haisam ban San sanda ka tafi ba, Amma ka shigo mota , mu ajiye ka gida."

"A a nagode, hanyata da Taki ba d'aya bace, Kuma na ma kusa Isa gidan namu baida Nisa da Nan" " Kar ka damu zamu Kai ka, komin kankancin nisan gidan naku" ganin tana neman takura shi, yayi tafiyar sa. Suman tsaye tayi tana bin shi da kallo, tana mamaki "wai shin Haisam wani irin mutumne haka?" A zuciyarta ta ayyana hakan, d'aga kafad'a tayi ta shige mota, d'aliban da suke gun Wanda suka ga abinda ya faru suna cewa ina ma ace sune Haisam, idan suka samu wannan damar baza su bari ya wuce su ba.

Bayan ya Isa gida ya tarar babu abinci a gidan nasu kamar kullum, uniform d'insa ya cire sannan ya nufi kasuwa don ya taimakawa mahaifiyar sa, Koko take yi da kosai dashi suke rufa wa kansu asiri, Bredi ta saya Masa, had'awa yayi da kosai yaci Shine abincin ranar nasa.

Da yamma, Kosai da doya ya d'auka a Tray ya fara talla a bakin titi, Yana cikin tallan ne ya hango wata mota kamar wacce aka Zo d'aukan Ma'isha da shi d'azu yayi saurin 'buya a bayan wani shago yana kallon motar ga mamakin saai yaga Ma'isha ce da mahaifiyar ta, sun Zo sayayya a kasuwar gwari. Kasa motsi yayi don baya son Ma'isha ta ganshi yana tallan Kosai a bakin titi, Ma'isha da mahaifiyar ta sun d'auki lokaci sosai Wanda hakan yasa shi kasa sakin jikinsa, Wani mutumi Wanda ya kasance kullum sai ya saya kosai da doya a gunsa ya hango shi ya shiga kiransa sunan sa Amma Haisam yayi burus kamar bai jishi ba,sabida idan yaje Ma'isha zata iya ganin sa.

"Ka kyale ni don ni ba zuwa zanyi ba,gara ma kayi Shiru " zancen zuci yake. Mutumin ya zago ta bayan sa,dafe shi yayi a kafad'a yace "Haisam lafiya kuwa? Ko Kuma ka kurmance ne?" "Eh kiyi hakuri nayi nisa ne a tunani" "Mene haka da har yafi kasuwancin ka muhimmanci? Ko da yake kosai zaka bani na naira saba'in sai doya na talatin" ba musu ya sauke tray din ya sa a bakin leda ya mika masa.

Bayan Ma'isha da mahaifiyar ta sun gama sayayyar da zasu yi a Lokacin gari har ya fara duhu, hakan yasa bai sayar da kosan ba, hakan yasa yaji duk ransa a 'bace. A hanyar sa ta komawa shagon su ya hango Ma'isha da mahaifiyar ta na sayan kosai a gun Mahaifiyar sa. Iska mai zafi ya hura ya kuma neman wuri ya 'buya.

" Wai meyasa mutanen Nan suke bina duk inda naje? Hmm Allah yasa ba kullum zasu Rika zuwa Nan wurin ba, mutuncina da Ma'isha take gani zai zube" ya fad'a a bayyane. Sai da ya jira suka tafi sannan ya Koma shagon, Mahaifiyar sa tayi matukar mamaki da ganin bai sayar da kosan ba.

Page 3 & 4

Da sassafe, Haisam ya shirya don zuwa tallan Kosai Kan yaje makaranta, yana kokari yaga ya had'a kud'in w.a.e.c dinsa , Amma Kan ya dawo daga talla lokacin zuwa makaranta har ya kure, a ranar ya shigo school a makare ya tarar ansa wa anda sukayi letti shara, bayan sun gama yayi saurin shiga aji yana hada zufa, cikin rashin sa'a ya tarar da malamin Mathematics d'insu a aji yace "Haisam Ahmad Umar, Why are you late to school and why are you sweating like a Christmas goat?" Yan ajin suka shiga dariya Ma'isha ce kad'ai batayi dariya ba don ita bata ga abin dariya anan ba, Haisam shiru yayi baice komai ba, sabida bai San me zaice Masa ba hannu ya Masa alamun ya shigo.

Lokacin break, Ma'isha da kawayenta suka nufo inda yake, suna rokon sa akan ya Kara musu bayani akan darasin da akayi dazu da safe, ya na cikin koya musu kwasam wayar Haneef ya soma ringing, Afnan 'daya daga cikin kawayen Ma'isha Tace "Haneef meyasa kake kokarin distracting din mu? " " How am I distracting you, wannan ba Lokacin break bane?" Cikin 'bacin Rai Ma'isha tace " Na lura kana da neman magana Haneef, Mr trouble" Haneef mikewa yayi ya ture Ma'isha ta buge kanta a bango, Haisam ransa yayi mugun 'baci bai tsaya wata wata ba ya tsinke shi da mari, fad'a Mai Karfi ya parke a tsakanin su d'aya daga cikin d'aliban ya Kai karar su gun Form master din su.

Zane su yayi sosai kana yasa su yanka ciyawa, Ma'isha da kawayenta suka Zo da niyar taimakawa Haisam, Amma yaki yace su taimakawa Haneef sabida shi aka bawa wurin noman dayawa sabida shine silar fad'an Ma'isha Tace "A'a baza mu taimaka Masa ba, shi ya jawo wa kansa jiki magayi, yaron yana da matsala sosai" " Ma'isha ba a Rama mugun ta da mugunta, da babu Wanda zai tuba ya gyara laifin sa, Dan Allah kuje ku taimaka Masa" " okay , zamu taimaka Masa Amma da sharad'i" " What? " " Sai dai idan zaka Bari driver na ya ajiye ka a gida" "Inaa bazaiyu ba, I won't, I can't, can't you see that my uniform is very dirty? " Afnan tace " that's even more you should allow her to take you home, bai kamata ka tafi acikin kaya Masu ditti haka ba" "Okay, agreed, na amince"

Ma'isha da kawayenta sunji dad'i sosai, yanda Haisam yace sukayi hakan sukayi suka taimakawa Haneef, abin ya bashi mamaki sosai, bayan sun gama yaje ya bawa Haisam hakuri, Haneef yace "am awfully sorry for everything, Dan Allah kuyi hakuri, all of you should forgive For all the trouble I caused, Dan Allah ku barb'e ni a matsayin aboki" girgiza Kai Haisam yayi yace "Kar ka damu komai ya wuce" Ma'isha zuwa tayi ta sayo musu ruwan sanyi duk suka Sha sannan suka koma aji..

Bayan an tashe su, Ma'isha babu inda bata duba ba Amma bata ga Haisam ba, taji ba dad'i, shigewa tayi mota ta wuce gida, bayan ta bar gun ya fito ya fashe da dariya "Hahaha come and take me home Mana, so kike kije Kiga gidan mu don ki gane cewar mu talakawa ne, inaa bazaiyu ba" sai da ya tabbatar Ma'isha sunyi nisa da barin gun, kana ya fito ya wuce gida.

WASHE GARI

Ma'isha na Isa school ta tinkare shi "Na tabbata kana sane kake guje min, But Haisam, meyasa kake guje min? Why are you hurting me like this? Bani da kowa shiyasa nake so ka zame min d'an uwa kwalli d'aya, please stop avoiding me Dan Allah." "Am sorry, kiyi hakuri, forgive me please" " You're forgiven, yau zamu Kai ka gida" "Dan Allah ki bar maganar kaini gida, akwai inda nake zuwa ne Kan na tafi gida" Kan ta bashi amsa principal ya shigo yace "Good Morning class, today is the last day for those who have not paid for thier w.a.e.c fees. starting from tomorrow , personally will be coming to send home any student who comes to school without his or her Money, have I made myself clear?" Duk suka amsa da "Yes Sir" bayan ya fita, Haisam kansa yasa a Kan benci ya shiga tunani mai nisa, har aka tashi bai kula kowa ba tunanin yanda zai samu kud'in ne ke damun sa.

"Yaya zanyi?" Zancen zuci yake "mahaifiya ta bata da Kud'in da zata biya min sannan Dangin Ubana Babu Wanda yake da niyar biya min, Ya Allah ka kawo min mafita" Ma'isha Tace "lafiya kuwa? Haven't you paid the money?" Haisam yace "yes but, I hope to pay soon" baya cikin yana yin magana da kowa. Ana tashi ya Kama hanyar gida shi kad'ai yake tafiyar. Ma'isha ta Shiga damuwa ta rasa abinyi daga bisani ta yanke shawarar bin Haisam. Sai da ta tabbatar driver d'inta bai ganta ba a silale tabi bayan Haisam amma Haisam bai San da cewar tana biye dashi ba, yana isa gida ya Shige, Murmushi tayi tace "Finally, yau nasan gidan su. Sai ta juya ta koma makaranta, driver yayi jiran Duniya bai ganta ba hakan yasa ya koma gida.

Ma'isha na zuwa taga wayam ba driver hakan ya tabbatar mata da ya tafi, bata da wani zab'i da ya wuce ta taka da kafa. Kan ta Isa gida mahaifiyarta ta shiga tashin hankali kasantuwar bata tab'a aikata hakan ba, ranta yayi mugun 'baci da driver sabida ya dawo ba tare da Yar ta ba, a tsawace tace "Idan wani Abu ya sami 'yata I'll make sure you spend the rest of you life in jail"

Cikina Rawar murya driver yace "Is not my fault Ma, na dubata ta ko ina a makarantar Amma ban ganta ba, sannan bata makarantar don nine mutum na karshe da ya rage a makarantar, Kuma har na bar gun ban ganta ba"

"Zaka yimin Shiru a wurin Nan ko Sai na buge maka baki? Kaje ka Nemo min 'yata." Kan ta karasa maganar da zatayi ta hango Mai gadi ma Bud'e gate,Yana Bud'ewa sai ta ga shigowar Ma'isha, da gudu ta nufi inda take.

Page 5 & 6

WASHE GARI

Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam.

Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?" Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa.

Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta.

Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday nBabu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti"

"Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje."

Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta.

Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka. Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta"

Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma"

"Yes Mommy"

"Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka"

Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa.ko Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?"

Murya na rawa yace "Tana Murmushi Mommy tayi tace "To ka kaimu mu ganta ko?"

Jiki na rawa ya shige d'aki Suma suka Mara Masa baya, Ma'isha kuwa sai Murmushi take har cikin ranta take jin dad'in ganin mahaifiyar Haisam na raye, suna had'a da Haisam kuwa kallon tuhuma yake mata,tana ganin haka sai ta Fara dariya kasa kasa. Banda tari babu abinda mahaifiyar Haisam keyi, cike da tausayi yace "Ki kimsa ta ku fito" hannun Haisam ya riko, sannan ya cewa Ma'isha "Daughter zo mu jira su a mota" ba musu ta bi bayansu,suna isa inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya.

Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba. Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida.

Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa"

"Ina sauraron ki"

"Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba, sannan Ina so a biya wa Haisam WAEC"

Murmushi yayi ya riko hannun ta yace "Madallah da samun mace kamar ki a rayuwa, tabbas ke d'in rayuwa tace, Maryam Allah ya Miki Albarka, a irin Rayuwar da muke ciki yanzu kowa kansa ya sani Amma ke kullum cikin taimakawa na kasa dake kike"

Murmushi tayi Tace "To mijina mene ne amfanin Kud'in namu? Idan baza mu taimakawa na kasa damu ba,Kuma na lura Ma'isha tana so a taimaka musu ne kuma ina matukar son farin cikin ta,nasan idan taji Haisam zai dawo gidan nan kuma taji za a biya Masa WAEC zatayi matukar farin ciki"

" Hakane Yar Albarka,Halin ki ta d'auko tana da tausayi sosai,ga son mutane"

"Kaji ka da wani zance kai ta d'auko dai"

"Zancen kike so,yanzu dai naji dukkanin maganar ki, Kuma zanyi yanda kike ce, Kuma Insha Allah zan rike Haisam tamkar d'ana, da niyata gidan nasu nake so a gyara musu"

"A a tun da ga nan Kuma gidan ya mana girma mu kad'ai, su dawo Nan kawai"

"To ba matsala, idan Allah ya Kai mu gobe zanje makarantar tasu na biya Masa, sannan ina so kije gidan ki d'auko mahaifiyar Haisam d'in, ban yarda ta 'dauko komai ba, Zan tura miki Dubu d'ari biyu, ki saya mata kaya, idan na nadawo zamu fita da Haisam d'in Shima na Masa sayayya"

Farin ciki da Murna yasa ta rungumi mijinta had'e da yi masa godiya, a haka sukayi bacci.Washe Gari

Daddy Kan yaje gun aiki ya biya ta makarantar su Haisam ya biya masa Kud'in WAEC harda NECO. Mummy na fad'a wa Ma'isha maganar da suka tattauna Akan Haisam da Umma tayi farin ciki sosai harda tsalle, tayi ta musu godiya da musu addu'a Wanda ya dace d'a yayiwa iyayen sa.

Tana Isa school a kusa sit d'in Haisam ta zauna, tunda ta lura shi d'in ba mai son magana bane Hakan yasa sai ya kulata take kulashi. Principal ne ya shigo yana Kiran sunan wa'anda basu biya Kud'in WAEC d'in su ba, ga mamakin Haisam har aka gama ba a kira sunan sa ba, hannu ya d'aga yace "Excuse me sir!!!

Yace "Yes"

Mikewa yayi yace "I haven't paid and you didn't call my name"

Cike da mamaki yace "You didn't pay? What's your name?"

"Haisam Ahmad Umar"

Ya shiga dubawa Bai ga sunan Haisam ba Yana duba list d'in wa'anda suka biya yaga sunan Haisam yace "Mr Man you already payed"

Cike da mamaki yace "I payed? But sir please can you check the date of the payment for me?"

"Sure"

Yana dubawa ya Maida kallon sa ga Haisam yace "It was payed today"Yana Kai Nan ya sa wa'anda basu biya ba a gaba har Saida ya kai su bakin gate ya jaddada wa Mai gadi Akan Kar ya bari su shigo ya koma ciki. Haisam mamakine ya rufe, a zuciyar sa yake fad'in "Wa ya biya min Kud'in nan?" Da sauri ya d'ago kansa ya kalli Ma'isha ita ma kallon sa take, murya kasa kasa "kin San wani abu Akan haka ko?"

Kai ta girgiza Tace "Ni ban sani ba" ta karasa maganar tana rufe bakin ta alamun dariya take son yi.

Cikin sanyin murya yace "Ma'isha Please"

Tace "Daddy ne ya biya"

"Dan Allah dagaske?"

"Uhmn gashi ka gani"

"Amma. "

Shigowar malamin sune ya Hana shi karasa maganar da yayi niya, suna fita break ya Shiga neman ta bai ganta ba, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah Allah na gode maka, yau Dole. Naje gidan su Ma'isha da Umma muyi musu godiya"

Ma'isha da tun d'azu take tsaye a bayan sa tayi gyaran murya Tace "Anya zuwa gidan mu zakuyi ko Kuma Zaku koma gidan mu?"

"Ok zuwa Zamuyi dai"

"Za dai ku koma gidan mu"

"Ban fahimce ki ba?"

"zaka fahimta idan driver yazo sannan ko ka gudu zamuje har gida mu d'auko ka" tana kainan ta ruga a guje, Yana Kiran ta Amma ina tayi nisa.
















Post a Comment

أحدث أقدم