Dangin Uba ( 15 & 16)


Dangin Uba


DANGIN UBA


Page  (15 & 16) 

Kallon Baffan sa yayi yace "Dan Allah ka tashi baffa meyasa zaka durkuwa a gabana bayan kana matsayin ubane a gare ni, Ni na yafe maka duniya da lahira, maganar gida Kuma na bar maka shi halak malak hatta company d'in da kake aiki a Cikin na mallaka maka. Malam hassan kirkirerren kuka ya Fara yi yana fad'in "Nagode, Nagode Haisam Allah ya maka Albarka" ya maida kallon sa ga Umma yace "Zainabu kiyi hakuri ki yafe min Dan Allah"

"Bakomai na yafe maka, Allah ya yafe Mana baki d'aya."

Duk suka amsa da amiin, Malam Hassan Banda godiya babu Abinda yake har suka fice daga gidan, Nan su Daddy suka shiga hirar su suna farin cikin nasarar da suka samu. Tana ganin shigowar sa ta mike tana fad'in "Daddy ya dai. Da fatan anyi nasara"

Murmushin irin zasu gane kuren su yayi yace "Yar daddy ai daddyn nakin ba daga nan, plan d'inmu zai Fara ne daga yau, na gama nawa saura naki. Murmushi tayi Tace "Insha Allah Daddy kasa ranka anyi an gama kawai"

"Allah ya miki Albarka Yar Daddy"

Ta amsa da "Ameen."

Umma da Haisam hankalin su kwance ko bakomai sun karb'i hakkin su, Basu da sauran damuwa a rayuwar su, duk wanni abu da suke bukata na jin dad'in Rayuwa suna dashi.Wannan KenanHaisam da Ma'isha shakuwace Mai karfi ta shiga tsakanin su tare suke zuwa makaranta su dawo tare, kullum Haisam ke Kai su school, ko da kuwa bai da lectures yakan kaita ta idan sun tashi ya koma ya d'auko ta wasu lokutan Kuma ya jira ta har sai ta gama su koma gida.Umma da Mummy komai tare suke hatta unguwa zasuje tare suke zuwa shopping, har kauyen su Mummy tare suke zuwa.

Haisam ke zaune a Cafeteria yana cin abinci,Yana jiran Maisha ta Gama lectures,cin abincin sa yake hankalinsa kwance yayin da d'ayan hannun sa yake Kan wayar sa, wata budurwa da baza ta haura shekaru 20 ba ta nufi inda yake, da sallama ta karasa inda yake a hankali ya dago kansa hade da amsa sallamar ta, kallon ta ya tsaya yi, Murmushi tayi Wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar fuskar ta Tace "Sannu dai Dai dai ta nutsuwar sa yayi ya amsa da "yauwa sannu da"

"Dan Allah idan baza ka damu ba zan iya Zama anan?" Tana nuna kujerar da ke fuskan ta nasa.

Yace "yes yes zauna Mana"

Tace "Nagode, ta jaa kujerar kana ta zauna tana Murmushi, waige waige ta Fara yi kana ta hango wata ta d'aga Mata hannu had'e da fad'in "Waiter!

Cikin sauri ta karaso inda take Tace "Welcome ma what will I offer you?"

Kallon Haisam budurwan Nan tayi da ya maida hankalin sa Kan wayarsa, Murmushi tayi Tace "Ki bani irin abincin da yake"

Haisam d'an d'agowa yayi ya kalleta ya girgiza Kai hade da Murmushi ya cigaba da cin abinci sa, ba a dau lokaci ba ta dawo plate d'in chicken and chips, tasa hannu ta karba. Ganin Haisam bai kulata ba tayi gyaran murya Tace "Ni suna na Aysha kaifa?"

Ba tare da ya d'ago ya kalleta ba yace "Haisam"

Tace "Wow Nice name, kai a school d'in Nan kake ne?"

"Yes"

"Wani department?"

"Medicine"

"Nima a medicine nake Amma ban tab'a ganin ka ba, Amma aji nawa kake?"

"200 level"

"Oh shiyasa ni a 100 level nake"

Yace "Maybe"

Duk maganar Nan da suke bai d'ago ya kalleta ba. Lalle gayen Nan akwai rainin hankali duk yanda nake so muyi Hira ya kasa sakin jikinsa, dama ance kyawawan mazan Nan haka suke da girman kai" duk maganar Nan a zuciyar ta take. Bata lura ba har ya Kira Waiter ya biya su kudin su ya Mike zai tafi, karar kujeran da ta jaa Ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula da murya mai d'an karfi Tace "Ina Kuma zaka?"

Kallon ta yayi cike da rashin fahimta yayi d'an Murmushi yace "Gida" ya juya zai tafi tayi saurin mikewa Tace, 

"Dan Allah ko zaka iya bani number ka?"

"Number ta Kuma?"

"Yes number ka"

" Da fatan dai ba laifi nayi bako?"

Murmushi tayi Wanda hakan yasa Beauty point d'inta ya nuna tace "A a kawai so nake muyi wata magana da kai idan bazan takura maka ba"

Yace "Ok" ya Mika hannun sa alamun ta Mika Masa wayar ta, cikin sauri ta Mika masa wayar Yana sawa ya Mika Mata ya fice daga gun, bata samu damar yi Masa Godiya ba, Yar karamar tsaki tayi Tace "Anya gayen Nan zai Soni kuwa. Komawa tayi ta zauna ta Fara cin abincin ta, Haisam kuwa zuwa yayi ya tarar da Maisha na tsaye a jikin mota tana jiran sa, ta had'a raai, tun daga nesa ya fara dariya don yasan ta dade tana jiransa tun Kan Aysha tazo dama ta kirashi yace mata sai yaga cin abinci tazo ta same shi Kuma Taki.

Yana karasawa yace "Yar karamar Kanwata har an fito?

Cikin Muryar Shagwab'a Tace "Ba a sani ba"

"Haba Mangana me yayi zafi wai fushi kike dani?"

"Nikam ka bud'e min na shiga so nake naje gida"

Kai kawai ya girgiza da kansa ya bud'e mata motar ta shiga sai turo baki take ita a lallai an bata mata raai, Yana shiga ya tada mota suka nufi hanyar gida, sai surutu yake Yana bata Labari bata kulashi sai da Tace Umm ko hmmm har suka Isa gida, suna Isa ta fice ta shige gida ba ta Tsaya jiransa ba kamar yadda suka Saba ba, mummy na ganin ta Tace "Ke Kuma yau ko sallamar ma baza ki iya ba"

Cikin sanyin murya tace " Sorry mummy na shafa'ane" wuri ta samu ta zauna tace "Mummy ina wuni"

"Lafiya daughter ya school d'in dai?"

"Lafiya Lau Mummy, ina Umma?"

"Tana part d'inta, yanzu ma tashi a inda kike zaune zatayi wanka zamu je saloon wanke Kai"

"Yauwa Mummy Nima zan biku"

"Ahhh yau Kuma ba yayan naki bane zai kai ki?"

"Yes zan biku"

Haisam da sallama ya Shigo mummy ta amsa har kasa ya tsuguna ya gaida ta kana ya nemi wuri ya zauna yace "Ni zan kai ki, aiki nane wannan"

Turo baki tayi Tace "Bana so zanbi su mummy"

Yace "In ko hakane baza ki ba don bazan bari ki fita a gidan Nan ba"

Mikewa tayi Tace "To an fasa wanke Kan" ta shige dakin ta, Haisam yace " Kin ganta ko" 

Mummy tayi saurin fad'in "no no ba ruwan nikam kun fi kusa in sa muku baki ku kunyata ni ba dani ba" ta Mike ta shige dakin ta itama Haisam Yar karamar dariya yayi ya bi bayan Maisha ya tarar da ita tana kwance a Kan gado tana kallon saman dakin.

Turo kofar yayi a hankali tasan ba mai shigowa sai shi hakan yasa ta juya Masa baya, Murmushi yayiw ya zauna akan couch d'in dake dakin ajiyar zuciya yace "Please princess kiyi hakuri duk da ban San laifin me nayi ba, don na tabbata fushin Nan da ni akeyi, Amma duk da hakan kiyi hakuri"

Ok? kawai Tace ba tare da ta juyo ba, tashi yayi ya zauna a Kan couch din dake fuskantar ta, Kama baki yayi yace "Laaa ila kuka Princess? Me yayi zafi har Haka Dan Allah ki fad'a min laifi me nayi haka. A zuciyar ta Tace "Taya za'ayi na fada maka cewar ganin ka da nayi da watane ya sani kuka? Taya za'a yi na fad'a maka cewar bana son ganin wata mace ta rabe ka? Taya za'a yi na fada maka ganin ka da wata da nayi cafeteria ne ya sani kuka?"

Cikin wani irin salo ya ambaci sunanta "Ma'isha! A hankali ta dago kanta ta sauke su akan kyakkyawar fuskar sa kasa jure kallon da yake mata tayi ta Kuma rufe idanun ta.

Yace "Ma'isha tell me please ko Nima so kike nayi kukan?"

Girgiza Kai tayi had'e da fad'in "A'a" 

Yace "To tashi ki zauna"

Ba musu ta tashi ta zauna yace "Princess ina jinki Dan Allah me ya same ki. Shiru tayi sai kokarin boye hawayen da ke idon ta take Amma ta kasa, daga bisani ta fashe da kuka Mai sauti. Haisam har cikin ransa baya jin dadin kukan ta, musamman ma ace shine silar kukan nata ajiyar zuciya yayi yace "Dan Allah Dan Annabi na roke ki fada min dalilin kukan naki , bana jin dadin ganin ki a hakan karya min zuciya yake Dan Allah kiyi shiru"

Bata ce mishi komai ba ta cigaba da rera kukan ta. Mikewa yayi yace "Shikenan tunda ban kai matsayin da Zaki fad'a min matsalar ki ba na kyale ki, sannan yanzu nasan matsayina a wurin ki" har yasa hannu zai bud'e kofar dakin yaji saukar Muryar Tace "Yaya kayi hakuri"

Murmushi yayi yasan hakan ne kad'ai zai sa ta kula shi, kin juyo wa yayi jin ta nufo shi ya hada raai kamar bai tab'a dariya ba Tace "Yaya na"

Joyowa yayi Yana kallon ta , kanta a kasa tana wasa da yatsunta yace "Uhmn ina jinki?"

"Kayi hakuri Dan Allah"

"Hakurin me Kuma? Ni baki min laifi ba, kawai dai yanzu nasan matsayina a wurin ki Ni ba komai bane a wurin ki"

"Wallahi Yaya ba Haka bane ba , wallahi bayan mummy da daddy bani da Wanda ya fika a wurin Kuma Kai ma ka sani"

"In da hakan ne kamar yanda kikace ai da zaki fada min matsalar ki, da Allah fa nake ta had'a ki tun a hanya Amma kin ki kulani Kuma a hakan Zaki wani cewa ina da matsayi a wurin ki? In dai da Gaske ki ke ki fad'a min abinda ya same ki"

Turo baki tayi Tace "Ba Kai bane"

"Bani bane me?"

"Ai Kaine ka shanyani nayi ta jiran ka, ga Rana"

Murmushi yayi ya jaa hancin ta yace "yanzu dama don wannan ne kike uban kukan nan?"

Ka ta d'aga Masa alamun eh, yace "Ai Saida nace miki kizo Kika ki zuwa, abinci fa nake ci princess, Amma kiyi hakuri na Miki laifi" yasa hannun sa biyu ya rike kunnuwan sa, Murmushi kawai tayi yace "Kin hakura? Idan baki hakura ba bazan sake kune na ba"

"na hakura"

Ajiyar zuciya yayi yace "Kai na gaji"

"Ladan rike kunnen ka da kayi da bai Kai minti daya ba har ka gaji. 

" Yes Mana da wahala fa"

Dariya tayi harda tafi Shima dariyar ya shiga yi yace "Zo mu je dining nasan princess d'in yayanta tana jin yunwa"

Tace "kamar ka sani Yaya"

Shima yace "Kamar ka sani Yaya" Yana kwaikwayon Muryar ta.

Dariya sukayi a tare suka fita, shigan su parlor yayi dai dai da shigowar mummy parlor baki a bude take kallon su suna Hira suna dariya Mummy Tace " ni da sani za'a Rina ai, mutum ya shiga tsakanin ku kunya zaiji sosa keya yayi yace "Mummy in gaya miki da kyar da makerkyasa na rarrashe ta"

"Yes to maza je ki d'auko mayafin ki mu je saloon din. Cikin Muryar Shagwaba Tace "A a mummy sai kun dawo Yaya zai kaini"

Mummy Tace "Kinci gidan ku ja'ira kawai Ni Zaki jawa raai" tsaki tayi ta fice a hanyar ta tafita suka hadu da umma hakan yasa suka juya kawai hannu Maisha da Haisam suka d'aga musu suna a dawo lafiya.

Mummy Tace "Yaran Nan sun maida mutane kamar kakannin su" Umma Tace "Bakamar Haisam bama sai a hankali. Mummy Tace "Kin samin son a gaba wallahi ke Sam bakya ganin laifin yarinyar Nan ko kadan"

"Hmm Hajiya Kenan ai ni gaskiya nake fad'a ke dai da son d'a ya rufe Miki Ido bakya gani" a haka suna Hira har suka Isa parking lot already dama driver yasan da fitan su yana hango su ya fito da motar a baya suka zauna, ya Danna wa motar key suka wuce saloon. Haisam da Maisha suna zaune a dinning tana cin abinci shi Kuma sai tad'i yake ta mata tana ci tana dariya har kamar zata kware, kwasam wayaey sa ta fara ringing hannu yasa a aljihun rigar sa ya zaro wayan ganin sabon number yasa bai d'auka ba, sai da aka sake Kira a karo na biyu yayi picking sallama yaji jin Muryar mace ya sa shi tunanin Wace ce wannan da zakin Muryar da bai tab'a jin irin ta ba, a ransa yake ayyana hakan, ta sake sallama a karo na biyu ya amsa bayan sun gaisa daga d'ayan 'bangaren Tace "Ka gane mai magana kuwa?"

Yace "A'a " a takaice.

Murmushi tayi Wanda Yana iya jinsa Tace "Nice na karb'i number ka dazu a Cafeteria dazu, ka tuna"

Yace "yes na tuna, ya kike? "

Tace "Lafiya, idan baza ka damu ba Dan In na so muyi wata magana dakai idan baka komai. For now am busy gaskiya sai zuwa anjima when am less busy I'll call you"

Tace "promise?"

" Yeah Insha Allah"

"Okay sai na jika"

Kiit ya katse wayar, tunda ya fara wayan hankalin Ma'isha yake kansa Tace "Yaya who is that?"

Yace "A friend"

Tace "Okay"

Yace "Yau ina Baki Labari. "

Nan suka cigaba da hirar su Saida ta cita koshi suka koma parlor suna kallon favorite series dinsu a zeeworld Mai sun I Do.


Post a Comment

أحدث أقدم