DANGIN UBA
Page (11 & 12)
Daddy Shima mikewa yayi yace "hakan na nufin ka santa Kenan. Malam Hassan Sai kallon sa yake ya kasa cewa komai, girgiza Kai daddy yace "calm down, calm down ka zauna". Jiki a sanyaye ya zauna Idon sa akan hoton Sai zare Ido yake Yana kallon Hoton, daddy yace "Na dad'e ina neman ka tsoratan da kayi hakan ya tabbatar min da maganar da Zainab ta fada min Akan ka gaskiya ce"
Murya na rawa yace "me me me ta taa fada maka? Kar ka yarda da ita makaryaciya ce"
"Give a good reason da zan gano cewar makaryaciya ce"
"Ashe dama tana raye ni na d'auka ta mutu"
Waigowa yayi, yayi tsaki yace "To hell with you mu had'u a kotun" Sai ya fice, motar sa ya shiga duk hankalin sa a tashe Sai zufa yake ta goge wa da hannun sa, farar shaddan da ke jikinsa duk ya jike, Kai tsaye gidan sa ya nufa, yana parking dakinsa ya shiga matar sa na ganin sa ta gane ba lafiya don ko sallama baiyi ba ya shige. Cikin sauri tabi bayan sa tarar dashi tayi a d'aki yana kaiwa Yana kawo wa, cikin nuna kulawa da damuwa Tace "Malam lafiya me ya Faru na ganka haka sai safa da marwa kake?"
Murya na rawa yace "Rabi akwai matsala, akwai matsala wallahi"
"Malam zauna ka fad'a min me ke faruwa?"
"Zama? Ai banga ta Zama ba, ina naga ta Zama bayan asirina yana kokarin tonuwa?"
"Asirin ka? Ban fahimta ba Malam me kake nufi da hakan?"
"Ashe dama Munafukar matar Nan tana raye? Ashe bata mutu ba ita da danta?"
"Yes ni da ido na, na gani to Amma abinda ya d'aure min Kai hakan na nufin fa basu cikin d'akin don Babu yanda za a yi su tsira gas fa nasa aka sa hatta Wanda yasa wutan ya mutu da idona na gani fa. Ka gani ko Malam tun wanchan lokacin na Hanaka Amma kaki ji, yanzu gashi wa gari ya waya"
"Rabi yanzu fa ba lokacin wannan bane " Nan ya sanar Mata yanda sukayi da Daddy, Rabi Tace "Malam ka maida musu dukiyar su, ai yanzu ka samu fiye da abinda ka samu agun su, idan ka bari ya kaika kotu duk abunda ka Tara za a Basu"
"inaaa bazaiyu ba kin San tsawon shekaru nawa na yi ina tara kud'aden Nan kuwa?"
" Ni kuwa na sani malam, ko dai barin garin zamuyi ne Kam?"
"ai cewa yayi ko na bar gari Sai ya Nemo Ni"
"Nikam wane ne haka? Da yake kokarin tozartamu?"
"chairman ne fa Mus'ab Aminu"
Zaro Ido tayi Tace "Eh lallai malam baka nemi zaman lafiya ba wallahi in dai baza ka maida musu ba, kasan mutumin Nan yanda yake da taimakon al'uma baya bari a cutar da kowa"
"Na San da hakan, dole zan nemi mafita amm"
Kwankwasa kofar da akayi ne ya katse maganar da yake niyar yi. Cikin tsawa yace "Waye anan nace Waye ne. Cikin sanyin murya Tace "Daddy wani mutumine ya kawo sako yace a baka"
Rabi Tace "Shigo"
Murya na rawa yace "yes nine"
ID card dinsu suka zaro suka nuna masa, "Yan sanda ne an turo mu da warrant arrest dinka"
"Ni Ni kuma, me me Kuma nayi?"
"Idan mukaje office zakaji koma mene ne"
Nan take suka zaro handcuffs suna kokarin Sanya Masa a hannun sa, cikin tashin hankali yake Kiran sunan ta "Rabi! Rabi! Da gudu ta fito ita da 'yayan ta guda uku, Yaran na kuka rabi ma na kuka, har suka fice dashi suka sashi a mota. Suna zuwa police station suka tarar da Daddy, mummy, Umma, Maisha da Haisam duk suna zaune, cike da mamaki yake kallon su, hannu Daddy ya daga musu hannu, gani nayi sun cire Masa handcuffs din.
"Alhaji dole nayi kaji abinda yake cewa fa, shi ya kashe min miji ya kwace dukiyar sa,sannan nima ya so kashe ni da d'ana Amma yana rayuwar sa hankali kwance"
Mummy Tace "Kar ki damu ranar Monday komai zaizo karshe insha Allah, ke dai kawai ki fad'i duk abinda kika sani shine kad'ai zai sa a mishi hukunci dai dai da abinda ya aikata. Haisam yace "Amma mummy bamu da wani hujja, kinsan komai sai da evidence karshe ma a nemi a karyata mu"
Daddy yace "matsala daya zamu samu shine evidence din da shi ya kashe shi Amma duk sauran zaizo Mana da sauki insha Allah, ku shiga mota mu tafi" mikawa Haisam key din motar akan ya jaa su, karb'a yayi duk suka shige, Kai tsaye gida suka nufo. Zaune suke a parlor,duk jikin su a sanyaye yake ganin kukan da Umma take yake ci yaki cinyewa Mummy Tace "Kukan na mene ne haka ya Isa Dan Allah"
Cikin shesshekar kuka Tace "Wallahi ina ganin sa hankali yayi mugun tashi, tsayuwar da yayi a gabana sai naga kamar Ahmad ne Kai hatta muryar sa ma irin ta Ahmad ce, Hassan ya cuce ni bazan taba yafe Masa ba" ta karasa maganar tana kuka, Haisam Tashi yayi ya fice, Kai Tsaye d'akinsa ya nufa da gudu Maisha ta bi bayan sa. Daddy girgiza Kai yayi yace "Allah ya kyauta" ya nad'e garen sa ya shige d'akinsa.
Murmushi kawai tayi tace "Ya Haisam kuka fa ba naka bane, addu'a ya kamata muyi Allah ya d'aura mu a Kan sa. Maisha ba kukan dukiyar nake ba ko wani abu ba a'a ganin Umma ta a cikin irin wannan halin shi yake tada min hankali ko kadan bana son zubar hawayen ta, ba sanin mahaifina nayi ba shiyasa bana jin kewar sa duk da cewar na San na rasa gata na Amma Umma itace uwata itace ubana bazan juri ganin ta a haka ba"
"I know how you feel insha Allah komai zai dai daita"
"Allah yasa."
"Ameen"
Ma'isha sai surutu take Haisam kuwa sai aikin kallon ta yake tun baya kulata har ya Fara kulata suka Sha Hira sosai, a yayin da Mummy na chan tana rarrashin ummu, wannan Kenan.
RANAR LAHADI
Daddy na zaune a garden Yana karanta jarida, yayin da Haisam da Maisha na daga gefe suna Shan hirar su, mummy ce ta fito cikin Sauri ta miko Masa waya tace "Tun dazu ake ta kiran ka da sabon number"
Karba yayi ya Kara a kunnen sa banji me akace ba ya Mike yace "okay gani Nan zuwa"
Mummy Tace "Ina Kuma zakaje?"
Bai Bata amsa ba yace "Haisam maza d'auko makullin mota akwai inda zamuje"
Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?"
Watan March 2022 ya kasance wata mara Dadi a gare ni a cikin sati biyu na rasa mutane na kusa dani.
Kakata ta rasu washe gari kanwar mahaifina ta rasu, basu cika sati ba cousin brother na da abokanan sa guda uku sukayi hatsari duk su ukun suka rasu, shiyasa duk na kasa typing naso ace kamun Ramadan na gama littafin Nan Amma kana naka Allah na nashi, dole zan dakatar da Rubutun sai bayan sallah insha Allah, Dan Allah kusa Yan uwana a addu'a, Allah ya jikan Musulmai idan tamu tazo yasa mu cika da imani ameen.
Page (13 & 14)
Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya. Lafiya Lau police station zamuje kar ki fada wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Maisha suka kalli Juna, Mummy tabe Baki tayi Tace "Allah ya kyauta." Ta shige cikin gida.
Basu zarce ko Ina ba Sai police station,bayan sun shiga ciki Kai tsaye office din DPO suka shiga bakin su d'auke da sallama,ga mamakin su suka tarar da Baffan Haisam a zaune a cikin office din, DPO ya nuna was daddy kujerar dake gaban sa yace "bismillah yallabai. Ba musu ya nemi wuri ya zauna, bayan sun gaisa DPO yace "Nasan kayi mamakin Kiran ka da nayie ko?"
Ya amsa da "Yes sosai ma"
Gyaran murya DPO yayi yace "Dama malam Hassan ne ya bakaci ganin ka shiyasa ma na Kira ka. Daddy maida kallon sa yayi ga Malam Hassan yace "Ina sauraron ka"
Malam Hassan yace "Na yanke shawara ne zan maida musu da dukiyar su" a gadarance.
Girgiza Kai kawai daddy yayi yace "Ni Kuma ban amince da hakan ba, a lokacin da nake ta bibiyar ka da ka dawo da duk abinda ka San nasu ne Amma kamin kunnen uwar shegu, maganar kotu Kuma bazan janye ba Sai munje. Malam Hassan yace "A lokacin da kace na bayar banji zan iya bane ba Amma a yanzu na shirya" Daddy ransa yayi mugun 'baci sabida ganin yanda malam Hassan yake magana a gadarance, mikewa yayi yace "Haisam tashi mu wuce gida" ya nufi kofar fita, DPO yace "Yallabai Dan Allah ka tsaya" waigowa yayi yace "Na tsaya nayi me da na San sabida Shirmen Nan ka kirani wallahi da banzo ba.
Malam Hassan Jin za'a raba shi da komai da komai ya Fara wiiki wiki da ido Nan take zufa ya Fara keto Masa duk da AC dake cikin office din, Chan ciki yace "Alhaji kayi hakuri Dan Allah" ya maida kallon sa ga Haisam yace yace "Dan Allah kasa baki Haisam.
Haisam dake tsaye Yana kallon su yace "Daddy mu saurare shi a gama abin Nan once and for all ko ba komai hankalin Umma zai kwanta.
Ajiyar zuciya daddy yayi ya koma ya zauna yace " Shikenan DPO wani formalities za a bi don a tabbatar da zai bada komai da komai don wallahi I don't trust him ko kad'an.
Kar ka damu yallabai zan kula da komai, Na maka alkawari Nan da 2 days zan kammala komai,amma zamu ciga ba da ajiye anan d'in ne ko Kuma mu sake shi. A a no need ai Ku sake shi" ya maida kallon ga Malam Hassan dake zaune a kasa ya nuna sa da manuniya yace "Mind you if try acting smart with me I'll deal with you and make your life miserable" Yana Kai Nan ya fice Haisam ya bi bayan sa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa gida.
Horn Haisam yayi Mai gadi yayi saurin bud'e musu kofa, parking lot ya nufa yayi parking motar, Mummy , Umma da Ma'isha na zaune a garden d'in gidan suna jiran dawowar su, daddy dakin sa ya wuce abinsa suna mishi sannu da zuwa ko kallon su beyi ba bare ya amsa.
Haisam kuwa inda suke ya nufa ya nemi wuri ya zaunan, Mummy Tace "Son lafiya me ya Faru ne haka na ga ran Alhaji a 'bace?" Gyara Zama Haisam yayi ya fara jero musu yanda sukayi a police station, tunda ya fara magana suke kallon sa har ya Gama Babu Wanda yace komai, Mummy girgiza kai tayi ta tashi ta shige cikin gida, dakin Daddy ta shiga taje tana ta aikin rarrashi.
Umma Tace "uhmm yaro yarone baza ki tab'a ganin abinda nake hangowa ba"
Haisam yace "Umma Me hakan yake nufi, kina nufin akwai wata matsalane idan akayi hakan. Babba ma kuwa Haisam, Baffan ka mutum ne Mai had'ari ni dukiyar Nan wallahi bataw dame ni ba , dama don kai ne nake so a karba maka hakkin ka, ina ji ajikina akwai abinda yake Shirin aikatawa"
Ma'isha Tace "Insha Allah babu ma abin da zai faru Umma, aniyar shi ya bishi"
Ta amsa da "Amin Allah ya shiga tsakanin mugu da na gari" duk suka amsa da Amin. Nan dai Haisam da Ma'isha sukayi ta kokarin jaan ta da Hira tun bata kulasu har aka fara hirar da ita. Ka gani ko malam ai tun farko Haka nace maka kayi Amma kayi kunnen uwar shegu da ma baza a kai Nan ba.
Kinga Rabi ni bana son Mai maita magana, Allah ya kaddara hakan Sai ya Faru in ma maganar kulleni da akayi ne ai ba yau na fara shiga cikin cell ba so Dan Allah ki kyaleni naji da abinda yake damina ko Kuma na sauke 'bacin ran a Kan ki. Rabi na jin hakan ta shi ta fice daga dakin ba tare da tace komai ba, binta yayi da kallo ya ja wani dogon tsaki. Dakinta ta nufa tana Zama Kenan taji an turo kofa, kallon kofar tayi ganin irin kallon da take mata tayi kirkirerren Murmushi Tace "Ayra Shigo ciki mana.
Wacce aka Kira da Ayra naga ta Shigo ta zauna a bakin gadon dake d'akin Tace "Mamy wai Dan Allah me ke faruwane, naga duk kina cikin tashin hankali, nasan hakan bazai rasa nasaba da Abinda ya faru da daddy bane ba, Dan Allah me daddy yayi har aka Kama shi. Babu komai Ayra, ai daddyn naku ma ya dawo komai ya Riga ya wuce kar ki tashi hankalin ki.
Amma Kuma Mamy ke naki hankalin ai a tashe yake just in 2 days ki duba Kika yanda Kika rame Kika lalace. Ayra kin San fa bana son ina magana Kuma kema kina yi sabida haka ko ki bar maganar Nan ko ki fice min daga d'aki bana son Shir. Me yasa baza ki fada mata ba, ai Ayra ba karamar yarinya bace ba, ta girma ya kamata ta San halin da ake ciki tunda baza ki iya sanar da ita ba Ni zan fad'a Mata. Wuri ya samu ya zauna, yace " Ayra" ta amsa da "Na'am Daddy"
"Kin tuna cousin brother d'inki Haisam?"
"Eh daddy d'an Uncle Ahmad"
"Good"
Nan ya shiga jero mata abubuwan da ya Faru shekarun baya kamo yanzu, Murmushin gefen baki tayi tace "Daddy wai dama suna Raye na d'aukan sun mutu fa"
"Suna Nan a Raye"
"To shi Alhaji Mus'ab d'in me had'in shi dasu da yake son taimakon su kalen dangi kawai"
"Ke ke ke, me haka nace me haka? "
Mikewa yayi ya nufe ta yace "So Kika kisa mata tsanata a ranta ko me kike nufi, wannan wani irin mumunar hud'uba kike Mata haka"
"Amma malam kasan"
Amma me, nace Amma me wallahi tallahi Rabi zan sab'a miki akan wannanw maganar wallahi daf kike da rasa auren ki. Mikewa itama tayi Tace " In rasa Mana ai auren Nan da shi da Babu duk daya"
Cike da mamaki yace "Oh haka ma Kika ce ko?"
"Yes Haka nace"
"toh Shikenan kije ki na sak"
Ayra Tace "No daddy kayi hakuri Dan Allah, kar ka aikata, Dan Allah kar ka saki mamy" ta karasa maganar tana kuka.Tsaki yayi yace "Kinci Albarkacin Ayra, Allah ya miki Albarka Ayra. Ta amsa da amiin, yace "Naji dad'in maganganun ki hakan ne yake kara tabbatar min da cewar bazan wahala wurin d'aukar fansan da nake sonyi ba, Akwai aikin da nake so kimin, idan Kika min hakan na yafe Miki duniya da lahira."
"Inshallah zan maka ko ma mene ne Daddy don samun albarkar ka"
"Malam kar ka saka yarinyar Nan acikin matsalar ka ka fama Kai kad'ai"
"No mummy mahaifina ne fa, matsalar da ai tawa ce, so kar ki damu"
Murmushi daddy yayi yace "Good My Girl wuce muje kafun tayi poisoning mind d'inki"
Ficewa sukayi a d'akin a tare suka bar ta ita kad'ai, Mamy ta rasa abinda yake mata dad'i, ajiyar zuciya tayi Tace "Ya Allah ka shirya min su ka ganar dasu gakiya.
*BAYAN KWANA BIYU*
Daddy na zaune a parlor shi da Haisam suna kallo suna Hira sama sama kasantuwar Yau lahadine yasa bai fita office ba, Mai gadi ya shigo bakinsa d'auke yake da sallama, suka amsa.
Cikin girmamawa yace "Yallab'ai kayi baki"
"Baki Kuma su wane ne Haka?"
"Wai DPO ne da malam Hassan"
"okay Ce musu su Shigo"
" To yallab'ai" ya fice.
Daddy yace "Son wai ina mutanen gidan Nan suke ne?"
"Suna part din Umma"
"Okay je ka Kira min su duka"
Mikewa yayi tare da fad'in "to daddy."
Tun daga bakin kofar parlor yake jiwo muryar su suna Hira suna dariya , da sallama ya shigo shima Yana daruyay duk da bai San dariyar me suke ba, yace "Nima nazo ne ayi hiran Dani"
Umma tace "A'a you're not welcome here, yau ranar ta Mata ne"
Yar karamar dariya yayi yace "Nikam dama nasan ba'a yina a gidan Nan Ma'isha kawai ake so"
Ma'isha Tace "Ji Yaya fa dan Allah ni Kuma me ye nawa acikin maganar ku?"
" Oh ma baki sani ba?"
"Eh ban sani ba"
"To ki taso Mana kawai ki shake min wuya na fad'a maki"
Taso wa tayi ta nufe shi tana dariya yace "Ki karaso Nan kiga abinda zan Miki"
Mummy Tace "Yaran Nan Basu da kunyan wallahi,Amma alhaji duk baya gani"
Haisam yace "Laaa Kinga na Manta wallahi daddy ne ma ya aikoni wai nazo na Kira ku"
Umma Tace " Kuma ka tsaya shirme ba"
Mummy Tace "Lafiya dai ko? Nifa bana son irin Kiran Nan"
Murmushin yayi Wanda ya kara bayyana kyawun fuskarsa yace "Lafiya Lau, Baffan hassane suka Zo"
Daddy yace "DPO shine kazo da kan ka? Ai da ka kirani zuwa office d'in"
" A a y'allabai kasan an rufe case d'in Kuma naga maganar yanzu na gidane ba sai a office zamuyi shi ba"
"Wannan ma hakane"
Mikewa DPO yayi ya Mika wa daddy wasu files, karb'a daddy yayi ya shiga dubawa, bayan ya Gama dubawa yace "Ka tabbata ka had'a komai da komai?"
Murya na rawa yace "yes Alhaji"
Daddy yace "Son Zo ka karb'a, har ya sa hannu zai karb'a yace "Daddy da dai ka bar su a wurin ka tukanna, Ni ban San me zanyi dasu ba a yanzu gaskiyane.
Yar karamar dariya daddy yayi yace "Son Kenan dukiyar kace fa, ba nawa ba"
"Yes na sani daddy shiysa nace ka rike su tukunna"
"A a son ba za a yi Hakaba"
Umma Tace "Alhaji haryanzu Haisam yaro ne ka rike d'in kamar yadda ya bukata"
" Toh Shikenan" Sai ya ajiye su a Kan side table dage gefen kujerar da suke zaune.
Ya maida kallon da ga DPO yace "Nagode sosai dpo Allah ya saka da alhairi"
"No Alhaji bakomai aikina kawai nake yi" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Mu tafi ko?"
Yace "Umm umm Dan Allah Alhaji alfarma nake nema a wurin ka"
"Babu wata alfarma da zan maka ka tashi ka fice min daga gida"
Mummy ce ta dafe shi a fad'a alamun plz ka saurare shi Sai Kuma yace "Fad'i ina jinka"
"Alhaji Dan Allah so nake a taimaka min da muhalli ko da gidan da muke cikine naci Albarkacin yayana Dan Allah, bani da inda zan zauna da iyalai na"
Kallon kallo a ka Fara yi a d'akin Haisam Kuma Murmushi kawai yayi.
Daddy yace "Hakan ba Mai yiwuwa bane ko da yake bani da iko da dukiyar nan, dukiyar Nan ta Haisam ce shi zaka roka ya maka wannan alfaramar bani ba.
Malam hassan har kasa ya durkusa a gaban Haisam yace "Haisam Dan Allah ka taimaka min , nasan ban chanchanchi yafiyar ka ba amma dan Allah find a place in your heart and forgive me. Haisam kallon Umma yayi da tun dazu take ta aikin kallon sa, Murmushi tayi shima ya maida Mata.

Post a Comment