Dangin Uba (19 to 20)


Dangin Uba

 

DANGIN UBA

Haisam na shiga parlor cikin girmawa ya gaidasu mummy suka amsa, Umma kallon tuhuma take Masa Tace "Haisam me kayi wa 'yata?"

Cikin rashin fahimta yace "Umma ce Miki tayi na mata wani abun.







Gidan ku Haisam ina tambayar ka kana maida min amsa da tambaya?"

"Wallahi Umma Ni ba abin da na Mata, sai dai Kuma in sharri ta fara yi"

" Wani irin sharri yarinya ta fita tana walwala da farin ciki ta dawo cikin 'bacin Rai ka dai.

Mummy ce ta dakatar da ita tace "Ki daina shiga maganar yaran Nan wataran Zaki ji kunyane To"

"To ai abun ne da mamaki daga fitan su ta dawo Haka?"

"Da dai kinyi shiru da kin taimaka wa Kan ki sabida kunya zakiji, Ni da ranar na shiga maganar su ba kunya tani sukayi ba, ina Nan ina goyon bayan Son Ashe ya lallab'a sun shirya, kawai nazo wucewa naji Muryar su suna Hira suna dariya tun daga Nan na fita harkan marasa kunya"

Haisam yace "Ma'isha dai akwai abinda ke damin ta nayi nayi da ita ta Sanar dani taki daga bisani ma kuka tayi tamin dakyar na rarrashe ta"

Mummy tabe baki tayi Tace " Kwaji dashi"

Umma Kuma Tace "Nikam ai baza taki Sanar dani ba" mikewa tayi ta shige d'akin Ma'isha ta tarar tana kuka ta kwanta ruf da ciki, Bata ma San da shigowar Umman ba.







Dafe ta tayi had'e da Kiran sunan ta cikin murya Mai sanyi "Daughter!!!

A firgice ta tashie ta zauna tasa hannu tana share hawayen dake fuskar ta, kirkirerren Murmushi tayi Tace "Umma kece ban ji shigowar ki ba"

Ganin irin kallon da Umma take mata yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsunta Umma tace "Ma'isha me ke damun ki? Yayan ki ya Sanar dani kina cikin damuwa Kuma kin ki fad'a Masa sannan yace min kina kuka na d'auka shirmen sane Ashe da Gaske ne tunda na gane wa Ido na, me ke damun ki? Ki saki jikin ki Nima tamkar mahaifiyar kice"

Murya na rawa tace *

"Babu komai fa Umma"

"Baza dai ki fad'a min ba, ko kina ganin ban Kai ki fad'a min bane?"

"A'a Umma har kin wuce ma, kawai ban San ta ina zan fara Sanar dake damuwata bane"

"ki fad'a min ta ko ina zan fahimta Kuma Insha Allahu zamu samu mafita"

"idan na fad'a mata dalilin kuka na tabbas nasan zata Sanar da Haisam sannan idan na 'boye Mata Kuma baza taji dadi ba Dole ma nasan yadda zanyi, na gwammaci nayi ta dakon soyayyar a zuciya ta har izuwa ranar da zai bud'i bakin sa yace Yana so na"

Dafe kafad'ar Ma'isha Umma tayi hakan yasa ta dawo daga tunanin da take Umma Tace "Ki Sanar dani matsalar ki"

"Umma Ina son... "

"Kina  son me?"

"Inaso na Sanar dake Amma this is not the right time idan lokaci yayi Zaki ji Insha Allah, Amma for now ina bukatar addu'ar ki please"

"hmmm Shikenan Daughter Allah ya yaye Miki damuwar ki"

"Ameen Umma"

"To tashi muje parlor muyi Kallo"

"Ya Haisam na parlor ne Umma?"

Mikewa tayi Tace "Dama zan karb'i sako a wurin sa"

"Ai na d'auka fushi kike da yayan naki"

"Umma ai ni da Ya Haisam sai Allah"

"Allah ya muku Albarka"

Ta amsa da ameen.

Suka fice, suna isa parlor ba taga Haisam ba Tace "Mummy Yaya na fa?"

Wani irin Kallo ta mata Tace "Sandan kiwon sa ya 'bata"

Turo baki tayi zatayi magana Umma Tace "Jeki d'akin sa maybe yana chan"

Tace "To umma" da saurin ta ta fice.

Mummy ta bita da Kallo kana ta maida kallonta ga Mummy Tace "Kinga abinda nake fad'a Miki ko?"

Umma Murmushi tayi Tace "Na gani."

Babu Wanda ya sake cewa komai suka cigaba sa kallon su.

Tun daga Baki kofar d'akin sa take ji yana waya yana dariya d'an tsayawa tayi Tace "Waye Yaya samu haka?"

Jin ya ambaci sunan Aysha yasa taji kamar an soketa da kibiya a kirji, shiru tayi har ta juya xata koma sai Kuma ta dawo ta bud'e kofar had'e da sallama, Yana ganin ta yace "Am Sorry zan Kira ki anjima" ya katse wayar, Ma'isha Murmushi tayi har cikin ranta taji dad'i ko ba komai tana da muhimmanci a gun sa, sai wata zuciya Tace Mata "idan Kuma 'boye Miki wani Abu yake fa?"

Yace "Princess ya dai kin tsaya kina kallona ki zauna Mana"

"Yaya meyasa ka katse wayar da kake yi?"

"Sabida princess d'ina ta Shigo lokacinta ne ba na kowa ba"

Taji dad'i sosai hakan yasa ta zauna Nan fa suka fara Shan hirar su sosai suna cikin farin ciki.

Aysha kallon wayan ta ke Tace "Ya Rabbi gayen Nan zai bani wahala, a hakan zan samu soyayyar sa? Amma ba komai insha Allah sai nasan hanyar da nabi na sa ka Fara Sona ko ta wani hanya ne.








MONDAY

7:45am

Kiranta yayi a waya murya cikin fad'a fad'a  yace "Wai me kike haryanzu ne? So kike na makara?"

"Am sorry gani nan "

Kitt ya katse wayar cikin sairi ta fito ta bud'e motar ta shiga tana Zama bata ma rufe kofar ba ya ya tada motar tana rufewa ya jaaa motar suka nufi hanyar school kana kallon fuskar  sa zaka gane ransa a 'bace yake cikin sanyi murya Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi na tashi da ciwon Kaine"

"Dama kin tab'a rasa abin fad'a ne? Inaga ma Dole na bar driver ya Rika kaiki aini ba driver d'inki bane ba"

"Yaya har abun ya kai ga Haka?"

"Wuce Nan ma"

"Ai Yaya naga lectures d'in naka karfe 8 ne Kuma haryanzu da sauran time"

"Malama test nake dashi  Kuma malamin Nan ba imani bane dashi, 8 na cika yake rufe kofa ba Mai Shiga ba Mai fita, sabida Kinga baki da lectures sai 9 yasa Kika 'bata min Lokaci"

"Wallahi ba haka bane Yaya"

"Hakane Mana, wallahi ki ka Kuma maimata irin haka tafiya zanyi na bar ki"

"Insha Allah bazan sake ba kayi hakuri"

"Da kuwa kin taimaka wa Kanki, don Kanki kika taimaka bani"

"Kayi hakuri"

"Naji" kawai yace Mata har suka Isa cikin makaranta babu Wanda ya ce uffan a cikin

Saida yayi parking Tace "Yaya ka saki ranka Mana in ba haka ba test d'in bazai maka dad'i ba"

"Kin San da hakan ai Kika bata min raai? Fita yayi a motar ganin zai iya kulleta a ciki itama tayi saurin fita jakarsa kawai ya d'auka a back sit yayi tafiyar sa ba tare da yace Mata komai ba.






Ma'isha mamaki ne ma ya kamata bata tab'a ganin sa haka ba, "ko da yake ni na 'bata Masa raai zuwa anjima nasan zai huce tunda hakan ba halin sa bane ba.

Haisam sauri yake sosai sabida saura minti biyu kachal time ya cika, Yana Shiga LT zaman sa kenan zai ga shigowar malami, ai kuwa yana Shiga yasa aka rufe Masa kofofin, Nan ya Shiga arranging d'insu zaman da sukayi babu Wanda zai iya magana da wani inko kayi za'a jika sanan baka Isa Kati satar amsa ba layin medicine ba wasa kwata kwata su sha Tara ne a ajin bayan mutum sama da talatin ne suka samu admission sauran tun a aji d'aya aka zubar dasu Kenan ba wasa.

Alhamdulillah test yayi wa Haisam dad'i mintuna 30 aka basu Amma shi a cikin sa'a ya gama cikin mintuna 20,bayan sun gama duk suka fita, wurin motar sa ya nufa jin an Kira sunan sa yayi saurin juyowa Murmushi yayi yace "Kaga manyan mutane"

"Su ku Kenan ko?"

Hannu suka Sha yanda samari suke Haisam yace "Ya test d'in dai?"

Yace "Alhamdulillah"

"Masha Allah, Allah ya bamu sa'a ya amsa da amiin.

Haisam yace "Dama cafeteria zanje ban samu na karya a gida ba muje Mana"

"Wallahi Nima ban karya ba muje d'in"

Sai da ya ajiye jakarsa a mota kana suka wuce suna tafiya suna Hira sabida dakwai d'an tafiya daga College of medicine zuwa commercial area.

Inda ya Saba cin abinci Suka nufa, as usual chips and chicken yace a kawo Masa, abokin tafiyar tasa Kuma ya ce Fried Rice suna cikin cin abincin su ya hango Aysha Wanda itama tana d'ago Kai Kennan suka had'a Ido dashi Murmushi ta sakar Masa Shima ya maida Mata.






Karasowa sukayi da ita da kawarta sallama sukayi suka amsa musu, Tace "Zamu iya Zama?"

Haisam yace "Bismillah Ku zauna"

Bayan sun gaisa Tace "Yallab'ai wannan kawatace Sunanta mardiya a pharmacy take"

Murmushi ya Wanda a ko da yaushe shine abun yinsa yace "Nice to meet you pharmacists"

Ta amsa da "Nice to meet you too"

Ya maida kallon sa ga Aysha yace "Yallab'iya wannan abokina ne sunan sa Farukh a medicine yake"

Yar karamar dariya tayi Yallab'iya da yace ne ya bata dariya Tace "Sannu Dr Farukh"

Zaro Ido yayi yace "Dr? Da saurana tukunna, cemin Farukh d'in ma kad'ai ya wadatar"

"Hahaha to shikenau Sannu Farukh"

Yace "Yauwa ai yafi dad'i ko? "

Dariya sukayi dukkan su, suna cin abinci suna Hira, wayar Haisam ce ta Fara ringing ajiye spoon d'in hannun sa yayi, Yana picking cikin Muryar Shagwab'a Tace "Yaya"

Ya amsa da Na'am "Princess"

Cikin sauri Aysha ta d'ago kanta suka had'a Ido da mardiya, ji tayi kanta ya fara sarawa a ranta take maimaita sunan Princess? Shin Yana da matane ko kuma budurwa,inaa duk yadda akayi budurwar sace taya ma za'ayi ace wannan yarin santalelen Saurayi ace bayi da budurwa? Lallai aikina ya jiku zanyi fafutakan neman soyayyar sa sannan ne rabashi da so called princess d'in nasa.







Haisam yace wayan sa yake hankalin sa kwance, tunda ya fara wayar bai daina Murmushi ba alamun Yana Jin dad'in wayan, yace "To princess kizo Mana ki sameni a cafeteria Sai kici abincin"

Dariya yayi yace "Na Amince zan saya miki duk abinda kikaso Kuma sai kin cinye ehe."

Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta karaso cafeteria dake dama ba wani nisa tayi ba tun daga nesa da ta hango Aysha taji gaban ta yafi a bayyane Tace "Itace na gansu tare ranar, ba shakka itace Aysha"

Ajiyar zuciya tayi Tace "Koma mene ne zanji gaskiyar a yau".

Post a Comment

أحدث أقدم