WASHE GARI
Kamar kullum a tare suka shiga school tun karfe 7 na safe, Yau Haisam ya Riga Ma'isha Gama lectures hakan yasa ya zauna zaman jiranta a Mango garden na cikin School.
Kiran Aysha ne ya Shigo wayar sa, picking yayi da sallama daga d'ayan 'bangaren ta amsa da "Wa'alaikassalam yallab'ai kana lafiya?"
"Ina lafiya ke fa?"
"Nima haka"
"Masha Allah ka Shigo kuwa?"
"Yes na Shigo"
"Ok please kana ina ne nazo na same ka"
"Ina mango garden"
"Okay muna kusa ma gani Nan karasowa"
Ya Masa da " okay" ya kashe wayan.
Girgiza Kai Aysha tayi Tace "Qawata Kinga bawan Allan Nan, Yana da wani habit d'in da bana so wallahi"
"Me Kenan fa?"
Mardiya Tace "It's not a big deal qawata tunda in Kika kirasa yana d'agawa Kuma yana sauraron ki ai Shikenan Kuma Nan gaba da kansa zai Rika neman ki"
Huci tayi tace "Shikenan tunda kince Haka shiyasa a ko wani lokaci idan ina bukatar shawara Kai tsaye ke nake nema nasan zan samu solution"
" I will always be here for you Qawata,yanzu dai tashi kije ki same shi before it's too late"
Aysha tace "I thought tare zamu"
"A a kaaai, kamata ai daga ke sai shi zaki fi fahimta" ta kashe mata Ido d'aya,duka Aysha ta Kai Mata ta kauce.
Mikewa tayi ta Masa sai anjimu da jaddada mata idan ta gama zata kirata sai su koma gidan tare,tayi tafiyar ta, ba d'au lokaci mai tsawo ba kasantuwar LT d'in da take da mango garden ba nisa hakan yasa tayi saurin Isa inda yake.
Da sallama ta karasa inda yake bayan sun gama gaisawa Nan ya mata umarnin da ta fito da handouts d'inta, Nan ya zari d'aya ya Fara mata tutorial d'in sunfi awa d'aya yana mata, Amma fa hankalin sa na Kan wayarsa minti minti yake dubawa daga bisani Tace "Akwai abinda kake jirane? Naga sai faman duba time kake"
"Hmmm eh, Time nake dubawa kar princess tayi ta jirana karfe 3 zata gama lectures"
Tab'e baki tayi Tace "Wai dole Kai Zaka kaita gida ne?"
"Yes Mana to wa zai kaita in bani ba?"
Ganin yanayin sa ya canza tayi saurin fad'in "Lallai kana ji da ita sosai Naga karfe 2 yanzu da sauran time ai"
Yace "yes gashi wayata ta kusa d'aukewa ba chaji Kuma na baro cable a gida Dana saka a mota, kar ta Kira bata same Ni ba"
Ta amsa da "Hakane"
Yace "Anyways mu cigaba ko?"
Ta amsa da "Ok"
Sun dad'e a zaune a gun ya d'auki wayar sa ya Danna yaga a kashe tsaki yayi yace "Damn it!!!"
Tace "Lafiya kuwa?"
Yar karamar tsaki yayi yace "Wayar ta d'auke"
"In time ne bari na duba maka a wayata"
Yace "Yauwa please duba min."
Aysha na duba time taga karfe 3 da kwata Tace Masa "2:30"
Zaro Ido yayi yace "Wai tun d'azun Nan 30 mints kawai mukayi?"
Tace "Yes"
"Lallai time baya gudu"
"Ko dai ka gajine? Mu bari sai gobe?"
"A a kar ki damu mu cigaba kawai."
Murmushin kyeta tayi ba tace Masa komai ba ya d'aura daga inda ya tsaya.
Ma'isha tafi minti 20 tana jiran sa, Kiran wayarsa take Amma switch off sai ta tuna tana da Number Farukh ta shiga dialling har kusa yankewa ya d'auka cikin Muryar ta mai dad'in sauraro Tace "Ya Farukh ina wuni?"
Ya amsa da "Lafiya"
cikin Muryar bacci, Tace "Am sorry kana bacci na tashe ka ko?"
Yace "Yes wallah but kar ki damu ya akayi?"
"Dama na d'auka kuna tare da Yayana ne"
"A'a mun rabu tun d'azu da mukayi sallar azahar but yace min zaiyi wa Aysha tutorail but ki kirasa ki ji"
Girgiza kai yayi yace "kishi kumallon Mata, Amma guy d'in nan don ya raina min hankali yace min ba Soyayya suke da Ma'isha ba mtss" ajiye wayar yayi ya koma baccin sa, Ma'isha kuwa Mango garden ta nufa dake tasan wurin zaman sa Kenan yawanci.
Tun daga nesa ta hango su suna zaune dai dai lokacin da Aysha take dariyan sunan wani scientist da ya fad'a dariya take sosai Shima ya fara taya ta a Fili Tace "Tutorial d'in kenan" har ta nufi inda suke sai Kuma ta Canza shawara ta koma, gate na makarantar ta nufa tana fita ta tari napep ta wuce gida, ita kanta taji ta wani iri sabida shine karo na farko da ta shiga napep sannan shine karo na farko data Koma gida ba tare da Yayan ta ba.
Kiran sallah da akayi ne Haisam ya Mike a zabure Aysha ma mikewa tayi tace "Lafiya?"
"Kamar kiran sallah fa nake ji?"
"Yes Kiran sallah ne"
Ajiye Mata handout d'in yayi da saurin ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, baki bta bud'e ta tsaya kallon sa har ta daina ganin sa bata bar mamaki ba, wa'anda suke zaune a gefen su Kuma suka tsaya kallon ta, tsaki tayi ta wurga musu harara da sauri suka kau da kansu Tace "magulmatan banza kawai Mtssw" ta d'auki Jakarta da handout d'in da Haisam ya ajiye ta bar gun.
Haisam wurin motar sa ya nufa duk a tunanin sa tana jiran sa, ganin bata Nan yace "to ina tayi ne?" Sa hannu yayi a Goshen sa yana ta waige waige bai ganta ba sai Kuma yace "Maybe bata zo ba nasan dai zata jirani"
Daga bisani ya shiga Masallaci don yin sallah, har ya idar ya dawo Bata Nan Zama yayii a motar har wuri ta Fara duhu, tsaki yayi ya jaa motar yabar gun.
Yana shiga gida d'akin ta ya nufa ya tura yaji a rufe, d'akin mummy ya nufa ya ga bata Nan, da sauri ya fice ya nufi part d'insu da sallama ya Shigo a tsatsaye ya gaida su yace "Mummy Ma'isha fa?"
Cike da mamaki suke kallon sa Umma Tace "Lafiyan ka kuwa meya same ka Shigo a rud'e Haka?"
"Umma banga Ma'isha ba, na d'auka ta dawone Kuma ban ganta ba"
Mikewa Umma tayi Tace "Shirmen banza Kenan dama ta tab'a dawowa ba tare da Kai bane?"
"Umma wall "
Mummy ce ta katse shi da fad'in "Son kasan dai baza ta 'bata ba ko? Ka Kira wayar ta man"
"Wallahi mummy wayata ce ta d'auke to nafi sa ran ta kirani ne bata same ni ba"
Umma ce ta zaro wayar ta dake chaji ta Shiga dialling number ta Amma switch off kallon Haisam tayi Tace "A kashe"
A tsawace Tace "To uban me kake jira anan? Kana ji an Fara Kiran sallar maghrib yarinyar Nan bamu San a wani Hali take ciki ba ka fita kaje ka Nemo min yarinya,Kuma wallahi kar ka kuskura ka ka dawo gidan Nan ba da daughter na ba kaji na Gaya maka."
jiki ba karfi ya Shiga d'akin sa , cable d'in wayar sa ya d'auko ya fice ya fad'a motar sa, wayarsa ya zaro daga aljihun wandon sa kana ya sa a chaji, zaro Ido yayi don ganin fuskar wayar tasa da kyau a bayyane yace "15 percent to ya akayi wayar ta d'auke?"
Tsaki yayi ya kunnata ya Shiga dialling number ta haryanzu a kashe, jaan motar yayi ya fita Masallacin unguwar su ya nufa yayi sallah, bayan sun idar ne ya Kama hanyar makaranta, duk inda yasan Ma'isha ke zuwa babu inda baije ba Amma Bata Nan, duk da cewar dare ne Amma Akwai student a school d'in.
Haisam hankali a tashe ya Shiga motar sa ya nufi gidan su Ameerah, Ameerah qawar Ma'isha ce tun a secondary school yakan kaita gidan idan sun gama hirar su ya koma ya d'auko ta, Kiran layin Ameerah yayi da yaw Isa kofar gidan su.
Mamaki ma abin ya bata sabida ba ya kiranta haka kawai sai da dalili, picking tayi bayan sun gaisa yake fad'a Mata yana waje had'e da tambayar ta suna tare da Ma'isha ta tabbatar Masa da rabuwar ta da ita yafi 2 weeks tun bikin kawar su da suka je yace "Ya Salam"
Cike da kulawa tace "Lafiya kuwa? Wani abun ne ya Faru?"
"Lafiya lau, sai anjima bari na wuce"
"Baza ka Shigo ku gaisa da Mama ba? "
"Zanzo wani lokacin ki gaishe ta" kitt ya katse wayar.
Ma'isha kuwa tana chan tana ta baccin ta, da sallati ta farka ta kalli agogon dake d'akin ta taga karfe 7 saura mikewa tayi ta watsa ruwa kana ta tayi alwala tayi sallah wani uban yunwa take ji hakan yasa ta nufi kitchen food flask ta bud'e, farar Shinfa ta gani ta bud'e d'ayan taga stew tsaki tayi Tace "Mutanen gidan Nan da shinkafa nifa in ba tuwo ba duk shirme ne" plate ta d'auko ta zuba, kujerar dake Kitchen d'in ta samu ta zauna sai da ta cinye abincin Tass har ta Kara tasha ruwa tayi hamdallah, tasa Kai zata fita suka ci karo da Mummy Tace "Sorry mummy ban ganki ba ne"
cike da mamaki mummy Tace "Ma'isha kece?"
"Yes Mummy"
"Yaushe Kika dawo?"
"Tun kan la'asar"
Mummy ta Shiga ta yarfa hannu Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Amma Ma'isha Allah ya shirye ki,Ashe dawowa kikayi Kika sa Yayan ki wahalan neman ki yanzu ga chan Umman ku ta Hana shi zaman gidan na tace kar ya kuskura ya dawo ba tare dake ba Ashe kina Nan kina ta baccin ki"
Turo baki tayi tace "To ai mummy "
"Ai mummy me ke? Ki fita daga idona Ma'isha wannan wani irin rashin hankaline, me ya sami wayar ki mukayi ta Kira a kashe?"
"Ka jimin ja'irar yarinya ki tadawa mutane hankali ba gaira ba dalili, dama kije ki Kira shi yanzu, tun d'azu yaron Nan baya gida gashi tun safe bai sa abinci a cikin saba kuka tafi makaranta ke Kuma kina Nan kin zauna Kinci abincin ki in ba mugunta ba"
"Mummy kiyi hakuri Dan Allah, wallahi na Kira layin sa ban same shi ba Kuma na gaji da jiran sa shiysa,Kuma na dawo a gajiye shiyasa fa na dawo gida Amma kiyi hakuri please"
"Dallah gafara ki bani wuri ko na had'a kanki da ginin Nan Mara hankali kawai"
Ficewa tayi da sauri don taga alama mummy zata iya buga Kan natan ta dad'e bata ga 'bacin ran mummy irin haka ba, da gudu ta Shiga d'akinta tana matsar kwalla, tana kunna wayar shigowar kiran Haisam ne ya shigo.
Haisam a kishingid'e yake a cikin motar, parking motar yayi a kofar gida ya kasa shiga cikin gida don bai San irin masifar da zai Sha a gun sa ba, ta dad'e baiga umman sa a cikin irin 'bacin ran Nan ba.
Jin Kiran ya Shiga ya zauna cike da kulawa yace "Princess Lafiyan ki kuwa? Kina ina nazo na d'auke ki?"
Cikin sanyin murya Tace "Ina gida"
Cike da mamaki yace "Gida wani gidan? Yaushe Kika dawo?"
"Gida man Ya Haisam akwai wani gidane bayan namu? Kuma tun kan la'asar nake gida"
FEDERAL LOW-COST
Ayra kwance take Akan lallausar katifan ta, da sallama daddyn ta ya shigo tana ganin sa ta tashi Tace "Sannu da zuwa daddy Ashe ka dawo?"
"Yes Yar daddy na dawo tun d'azu mummyn ki Tace min kina school, ya school d'in dai?"
"Lafiya Lau daddy"
"Komai normal ko?"
"Yes Daddy"
"Masha Allah, to ya maganar mu ta kwana? Da fatan kin Fara aikin da na saki?"
"Hmm daddy Kennan ka kwantar da hankalin ka alkawari na maka sai na Kai makiyin mu kasa ko ta wace hanyance Kai dai kawai ka tayani da addu'a"
"I trust you Yar daddy, I trust you shiyasa na saki wannan aikin sabida nasan Zaki iya but mind you kibi a hankali kar kaikayi ya koma Kan mashekiya"
"hahaha insha Allah ba za'ayi hakan ba daddy your girl is very smart"
"Allah ya dafa Miki"
"Ameen daddy nagode, Ina tsarabata?"
"Yana Nan Zo muje ki karb'a"
Cike da murna ta Mike ta bi bayan sa.
Bayan ta karb'o ledan da ya Mika ma ta ta nufo d'akin ta, ji tayi an Kira sunanta cikin sauri ta juya don ganin Wacce ke kiranta ganin mahaifiyar Tace tayi Murmushi Tace "Na'am Mamy"
"Zonan ina da magana dake" tana Kai Nan ta shige d'akin ta Ayra ma tabi bayanta.

إرسال تعليق