DANGIN UBA
Hannun ta ta sauke daga kirjin ta, ta sauke ajiyar zuciya Tace "Kai Yaya ka tsoratani yaushe ka Shigo?"
Tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake yana kallon cikin idonta tabbas ta tsoro ta, yace Mata "Yanzu na Shigo, Ashe dama kin ganni?"
Kawar da kanta tayi kamar bata ji abinda yace ta hard'e hannun ta, ba ganin bata da niyar bashi amsa ya taso ya nufe ta, dab da ita ya tsaya ganin har yanzu bata kula shi ba ya hannu ya riko hannayen ta, wani abu taji yarrrr tun daga tsakiyar kanta I'xuwa tsakiyar kafan ta, da sauri ta zare hannun ta.
Murmushi yayi yace "Princess wai haryanzu fushi kike dani?"
Idonta cikin nasa, idanun ta sun taro ruwa kiris suke jira su zubo ganin hakan yaji duk ba dad'i kasa da murya yayi yace "I Know I hurt you, Dan Allah ya Isa Haka bana jin dad'in hakan duk kin Canza min kamar ba princess d'ina ba"
Hawayen da dama jira suke suka fara bin juna suna sauka da sauri yasa hannu yasa ya fara share mata yana girgiza kansa, ya kuma cewa "Am sorry My princess"
Ma'isha runtse idanun ta tayi tana Jin dad'in sunan My princess wani 'bagaren Kuma ji take kamar zuciyar ta zata fashe sabida gani take kalmominsa na yaudara ce kawai.
Riko hannun ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado, ya durkusa a gaban ta hannun ta d'aya ya rike yasa hannun ta a tsakiyan hanyen sa, murza hannun nata yake a hankali yana kallon ta, banda hawayen dake zubiwa daga idanun ta Babu abinda take yi, har sai da ya ga ta daina kukan ya sake hannun nata sannan ya mike ya zauna a gefen ta.
Still yana kallon ta yace "Please ki daina kukan haka bana son ganin ki haka, sannan dama na kawo miki labari ne Mai dad'i Amma na fasa" ya karasa maganar kamar yaro d'an shekara 3.
Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Na daina kukan fad'a min me ya faru?"
"Zan fad'a miki but da sharad'i"
"Ina jinka"
"Sai kin min alkawarin kin daina fushi dani tukunna zan Sanar dake"
" Yes ai Yaya Kaine kake fushi dani bani ba, tunda ko magana ma ka daina min ko da na maka ma amsa mara dad'i nake Samu ko Kuma kaki kulani, Kuma in ba Ni na maka magana ba bakayi min"
"I Know, kin 'bata min raai ne wallahi, Amma yanzu komai ya wuce am sorry kinji?"
"To Shikenan"
Mikewa yayi Tace "Haa'ah ina zuwa Kuma?"
"Sallah zanyi kema na San bakiyi ba, so ki tashi kiyi"
" Labarin da kace zaka fad'a min Kuma fa?"
"zan fad'a miki anjima ki tashi kiyi sallah, bye" ya d'aga mata hannu kana ya fice.
Haisam Bayan yaje Masallaci ya dawo ya koma d'akin sa yayi wanka, wando three quarter baki ya saka sannan ya saka Riga armless Shima baki kana ya fito yazo part d'insu Daddy zaman sa ke da wuya daddy ya Shigo da Baki sun Kai su Shida cikin girmawa ya gaidasu suka amsa, Kai tsaye dinning suka wuce, mummy da Umma suka fito daga kitchen da sauran abincin Nan aka Shiga gaishe gaishe, Bayan sun ajiye suka koma d'akin mummy suka fara hirarsu a chan.
Bayan su Daddy sun gama cin abinci suka d'an zanta har karfe takwas da rabi kana suka gama meeting d'in, fita sukayi duka a tare har wurin motocin su ya raka su duk suka wuce Amma banda mutum d'aya a tare suka sake shigowa a parlor suka zauna Haisam ya musu sannu suka amsa Nan fa daddy suka fara Hira ba kakkautawa da mutumin nan.
Ma'isha kuwa Saida tayi sallar Isha kana ta fito daga d'akin doguwar Riga ce Mara nauyi sannan ta saka baby hijab ta fito parlor ganin su daddy da gudun ta karasa inda suke ta fad'a jikin Daddy tana fad'in "Daddy sannu sa dawo wa"
Ya amsa da "Yauwa Daughter."
Dariya sukayi mutumin nan da suke tare da daddy yace "Oh daddyn ki kawai Kika gani baki ganni bako?"
"Laaah Abba wallahi ban gan ka ba, ina wuni?" Ta d'an duka ya Masa da "Lafiya su Isha manyan mata kaga yarinyar Nan yanda ta girma"
Daddy ya amsa da "Wallahi kuwa kasan girman mace"
"girman mace ai kamar Taki ake saka musu, ya school d'in dai dafatan ana kokari?"
"Yes daddy Alhamdulillah"
"Allah ya taimaka"
"Ameen nagode Abba"
Wanda ta Kira da Abba ne ya Kara maida kallon sa ga Haisam a karo na sau ba adadi ya maida kallon sa ga daddy yace "Yaya ina ta zuci zucin tambayar ka wane ne wannan?"
Murmushi daddy yayi yace "Ai shine yaron da nake baka labarin sa kwanaki"
"Ok" girgiza kai yayi alamun ya tuna kana ya d'aura da fad'in "Haisam ko?"
Yana kallon Haisam d'in, cikin girmawa Haisam yace "yea yallab'ai"
Murmushin gefen Baki yayi yace "Yallab'ai Kuma Haisam Kuma ka Kira Yaya na da Daddy? Ko Ni ban Kai a kirani da Daddy bane?" Ya karasa maganar a sigar wasa, sosa keya Haisam yayi yace "A'a ba Haka bane"
Gyara Zama Abba yayi yace Sunana Abdallah Aminu Tahir, d'aga Malam Tahir Mus'ab wannan da kake gani. Yana nuna daddy haisam ya kalli daddy kana ya maida kallon sa gare shi,ya d'aura da fad'in "Yaya nane uwa d'aya uba d'aya muke dashi shi ya sha nono ya bar min kaga Kennan Ni Abban Ma'isha ne zanzo ka Kirani da Abba kamar yadda Isha take Kirana"
Murmushi Haisam yayi yace "Insha Allah Abba"
Daddy Har cikin ransa ya ji daddy, hakan zai tabbatarwa da Haisam ya zama d'an gida.
Daddy yace "Daughter jeki ki Kira su Mummyn ku"
Mikewa tayi had'e da fad'in to, tana Shiga d'akin da sallama ta Sanar dasu cewar daddy na Kiran su a tare suka fito, gaisawa suka Kuma yi Nan sukayi ta Hira tare yayin da Alhaji Abdallah sai Satan kallon Umma yake ta lura da hakan, hakan yasa duk take jinta wani iri, sai da karfe 11 tayi ya mike da zummar zai tafi daddy da mummy sukayi duk yanda sukayi suka sa ya Kwana.
TSOKACI
Shin wane ne Alhaji Mus'ab Aminu?
Tun daga sannan mahaifiyar su ta kwanta rashin Lafiya yau da lafiya gobe ba lafiya a haka har ta shekara daga bisani ita ma ta rasu, da Taimakon Allah da na Mus'ab ya farfad'o da business d'in mahaifin nasu har ya samu Abdallah ma ya Zama mutum Shima ya fara business d'in.
Tare suke koman su har suka samu sukayi aure, a Rana d'aya suka yi aure, Shi Mus'ab Yar Gombe ya samu ya aura Mai suna Maryam, shi Kuma Abdallah a yawon business d'insa ya had'u da fauziya, fauziya bahaushiyar kano ce, Bayan shekara biyu Fauziya ta haifi d'a na miji sai yayi wa Yayan sa Mus'ab takwara, Bayan shekaru uku ta haifi Yan biyu dukka mata wata hassana da Hussaina,daga Nan suka koma Kano da Zama sabida ya cigaba da lura da business d'insu na Kano d'in.
Maryam hankalin ta kullum a tashe yake bata da wani buri da ya wuce ta samu ciki, kullum cikin kuka take Mus'ab shine Mai rarrashin ta.
Cikin Muryar kuka Tace "Mus'ab Zaka rabu har dani ko? Ko Zaka karo min kishiya"
Rungumeta yayi tsam a jikin sa yace "Bani da wacce ta fiki maryam, bazan tab'a miki kishiya ba insha Allah, kullum ina fad'a miki ki daina tada hankalin ki shi fa Haihuwar Nan na Allah ne.
Bubbuga Bayan ta yake yace "Amma ai ba dabarar ta bane Kuma kema ba laifin ki bane, tunda munsha zuwa asibito ci da dama har kasar waje munje duk zancen d'ayane dani dake duk bamu da matsala Kinga Kenan lokacin Haihuwar ne bata Zo ba, ki daina tada hankalin ki mu cigaba da addu'a"
AFTER 10 YEARS
Maryam ta tashi da zazzabi Mai zafi banda amai babu abinda take, cikiin tashin hankali ya kaita asibiti, Likita ya Sanar dashi labari Mai dad'in da ya dad'e yana son ji, farin ciki fal ransa ya Kira Abdallah ya Sanar dashi, dashi da Fauziya sunyi muran matuka, Bayan wata 9 Maryam ta sami yarta, yarinya kyakkyawa kama take sak da ubanta Amma da d'auki hasken fatar Maryam, kasantuwar Mus'ab ba wani haske yake dashi sosai ba.
Abdallah najin labarin Haihuwar ya sa suka shirya dashi da matar da yaran sa hud'u , Mus'ab, hassana da Hussaina sai Autan su Faisal, Wanda a lokacin Mus'ab nada shekaru 10, Hassana sa Hussaina 8 years sai Faisal a lokacin bai cika shekaru 4.
A Ranar suna Mus'ab ya Sanar musu da yarinya taci sunan mahaifiyar su wato Maryam Amma ana Kiran ta da Ma'isha, tun da sassafe suka shirya suka Kama hanyar Gombe a hanyar su ta zuwa gomben sukayi hatsari,Fauziya da 'ya'yan ta duk 4 suka rasu,yayin da Abdallah ya bugu sosai Yana kwance a asibiti Rai a hannun Allah.

Post a Comment