Dangin Uba (43 to 44)


Dangin Uba

DANGIN UBA

She?" Aisha keyi wa Daddy ta da yake tuki tayi wa wannan tambayar, cikin inda inda yace "Don't mind them please,shirme ce da irin sharrin su da suka Saba"

"To Shikenan, Amma daddy har naji tausayin sa Wallahi, Ya haisam na da kirkii Sosai"

Taka birki yace "Tausayin, Tausayi Kika ce" 

Ganin yanda ya ke zaro Mata Ido kana Yana maganar cikin fad'a ya tsorata tata Sosai.

Murya na rawa Tace "Am sorry"

Tsaki yayi yace "You better be, Banda wawiya irib rashin mutuncin da ya min baki ji tausayi na ba sai Tausayin sa? Kuma kul na sake jin kin ambaci sunan sa sai na sab'a miki shasha kawai"

A dai dai Nan suka Isa gida zata fita yace "Dawo Nan" Dawo wa tayi ta zauna bata ce Masa komai ba, ganin bai yi magana ba Tace "Daddy gani"

"Mis ai na zaci Zama zakiyi kina Kallo na tunda na Zama sa'an ki, kina jina?"

Ta amsa da "yes daddy"

"Good, Kar ki kuskura naji kin fad'awa maman ki maganar Nan"

"Yes"

"Wuce ki fita min a mota."

Tur baki tayi kana ta fita, likowa yayi yace "Ni kike turawa baki ina zan Shigo gidan na same ki Sai na ci mutuncin ki"

Da guda ta shige gida, shi Kuma ya fita daga gidan.





Bayan farfad'owar Abba da umma, Tunda mummy ta fad'a mata cewar Haisam ya Shiga comma ta bud'e sabon babin kuka Daddy kuwa yayi ta fad'a Yana fad'in "Ai dama sai da na Hana ki fad'a mata Amma kinki ji, yanzu ki ga halin da Kika sata a ciki"

Abba yace "haba Yaya ya Isa haka Mana tun d'azu kake ta fad'a Kuma, ai dama Dole ta sani ko idan bata sani ba Dole gaba zata sani so ni Banga abun tashin hankali anan ba"

Shiru kawai yayi bai ce Masa komai ba, Ma'isha na farfad'owa Meerah ta gani a gefen ta, da taimakon Meera Isha ta zauna abinci ta bata da ruwa da kyar ta karb'i spoon 3 ta Sha ruwa, ta tashi zata fita, Meerah ce ta rike ta had'e da fad'in "Ina Kuma zaki?"

"Gun Ya Haisam"

"Amma"

Dakatar da ita tayi da fad'in "Yanzun ma hanani ganin sa zakuyi? Bayan d'azu maganin bacci kuka bani?"

Sake ta tayi kana Tace " ya akayi Kika sani?"

"uhmn Kar ki manta fa Ni pharmacists ce nasan drugs" tana Kai nan ta fice d'akin da Haisam yake ta nufa taga wayam.

Da sauri ta fito ta hango Bayan Meera Kiran sunan ta tayi ta tsaya, su Daddy najin Muryar ta Duk suka fito , da sauri ta Karasa inda take Tace "Ya ban ganshi ba?"

"To ta ya za'a yi ki ganshi ce miki akayi ya shiga comma to where do you expect za a Kai shi pharmacists?"

"Or so that's mean yana ICU"

Hannu ta d'aga mata alamu oho, ta juya tayi tafiyar ta tana ganin su Umma ta nufi inda suke, dukannin su Sannu suke Mata ta amsa.

Abba ne yace "Ya kamata mu koma gida ko tunda duk Mun farkafarka.





Umma Tace "A bar Haisam d'in dawa?"

Ma'isha Tace "Umma Kar ki damu ina Nan, Kuma baza a bari a Rika Shiga kansa ba , kin san ba'a son motsi ko kad'an a ciki"

"Hakan na nufin bazan sake ganin sa ba ko?" Ta karasa maganar tana matsar kwalla, Ma'isha rungumar Umma tayi Tace "Please Umma ki rage kukan Nan haka Kinga nima na daina ko muyi ta Masa magana, Kuma Insha Allah zan nemi hanyar da Zaki Rika ganin sa lokaci zuwa lokaci, Kuma fatan mu shine Kar ya d'auki tsawon lokaci a ciki"

Mummy Tace "Allah yasa hakan ne don nifa Sam ban yarda da likitocin Nan ba, a Haka sukayi wa wata makwanbciyar mu ba Ashe kashe ta sukayi ance fa yawanci likitocin Nan mayu ne"

Ma'isha tayi saurin fad'in "La mummy Kenan Nima mayya ce ko?"

Duk sukayi dariya a Haka suna Hira har suka fita, Umma da Abba suka Fara ajiyewa a gida kana su  daddy suka wuce gida.

"Qawata ya akayi haka? Meyasa zakiyi wa Haisam haka? Dama ba son shi kike da Gaske ba?"

Mardiya ke yiwa Ayrah wannan tambayar, mikewa Ayrah tayi Tace "Na fad'a miki kwanaki a kwai wani buri nawa Wanda nake so na cika, Wanda Wannan burin nawa burin mahaifinane, Wanda na cika Masa burin sa Amma na rasa dalilin da yasa bana farin ciki da hakan"

Amma "Ayrah me ya Kai ki aikata irin Wannan d'anyan aiki tunda kinsan ba auren shi zakiyi ba, me yasa Kika had'a harda asiri?"

"uhmn Qawata Kennan to ai da ba don ke ba ai bazan samu damar Shiga ransa ba, kinga Kenan amfanin bokan Kenan ko"

Mardiya mikewa tayi cikin rashin fahimta Tace "I don't get you please ki Kara min Karin haske Akan abinda ban sani ba.





"zauna kiji" Zama sukayi Nan ta Fara Sanar da ita duk abinda mahaifin ta ya Sanar da ita da hanyan da tabi har akayi maganar aure, Kama baki Mardiya tayi Tace "Innalillahi Ayrah Amma gaskiya banji dad'i ba Kuma Ni gaskiya ina kokonta Akan maganganun kin Nan Haisam Sam bazai aikata hakan ba"

Rai a d'an 'bace Ayrah tace "Kina nufin kice Daddy na makaryaci ne?"

Cikin inda inda tace "A'a Ni Sam ba Haka nake nufi ba Amma. "

Murya Mamy sukaji ma'ana mahaifiyar (Ayrah) tana fad'in "Tabbas karya ya miki"

A razane ta Mike jikinta na kyar ma Tace "Mamy dama... dama kina Jin mune?"

"Kwaraai Yanzu ke Ayrah kin kyauta wa Kanki Kenan? Ashe dama abinda kuka aikata Kenan ko da yake Banga laifin ki ba kina amfani da abinda mahaifin ki ya d'aura ki a Kaine, to bari na fad'a miki gaskiyar maganar, mahaifin ki shi ya kashe Yayan sa, sannan ya kwace komai da komai nasa" Nan ta Sanar da ita komai da komai harda yadda ya aika a kona Haisam da mahaifiyar sa.

Ayrah Zama tayi a kasa, kasa motsi tayi sai hawayen dake gangarowa daga fuskar ta bakin ta rawa ta ma rasa me zata ce, Mardiya ce ta karasa inda take tasa a hannu ta d'aga ta ta zaunar da ita a kan gado fashewa tayi da Kuka tana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un me na aikata wa kaina, me nayi na Shiga uku" 

Tsaki Mamy taja Tace "Kuka ba? Baki ga komi ba tunda kin biye wa ubanki zaki ji dashi" tana Kai Nan ta fita, Mardiya ce tayi ta rarrashin ta tana Jin jina lamarin tabbas mahifin Ayrah abun tsorone.

Aisha tun daga Wannan ranar ta Shiga tashin hankali mara misaltuwa tundaga wannan ranar take kiran layin Haisam Amma baya Shiga tayi kuka tayi kuka har ta godewa Allah.






Yau ta kudiri aniyar ko ta halin Kaka sai ta ganshi, har asibitin da yake aiki taje aka tabbatar mata da bayi da lafiya, jiki ba karfi ta fita a hanyar ta ta fita sukayi kicibus da Farukh.

Farukh na ganin ta ya kawar da kansa Kamar bai tab'a ganin ta , da sauri ta bi Bayan sa tana Kiran sunan sa baiyi niyar kulata ba ganin yadda take kiran sunan da ya ja attention d'in Mutane yasa ya tsaya, kallon ta yayi kana ya kawar da kansa had'e da fad'in "Lafiya kuwa kike ta bina?"

"Am Lafiya lau dama Kaima anan kake aikine?"

Kallon ta yayi yasa hannu a aljihun wandon sa kana yace "umm umm a specialist nake, tambayar Nan ce ta sa Kika tsayar Dani?"

Jiki a Sanyaye Tace "A a dama ina Kiran layin sa ne baya Shiga shine nazo neman sa aka ce min bayi da lafiya me ya same sa ne Haka?"

Ciza leb'en sa yayi cike da takaici yace "As if you care ta ina ruwanki da lafiyar sa bayan burin ki Kenan? To Haisam ya Shiga comma a dalilin ki kinyi farin ciki ko? Mis" ya tafi ya barta a tsaye a gun baki a bud'e.

Ta dad'e a tsaye a gun kana ta wuce gidan su mardiya ta sanar mata da halin da Haisam ke ciki "tab wai yanzu a dalilin ku, a gaskiya Wallahi Allah bazai bar ku ba, idan kuma ya Rasa ransa a dalilin ki kema kin Zama Kamar mahaifin naki"

"look mardiya nasan mahaifina ba mutumin kirkii bane ba, Amma that's not give you the right to disrespect him kin gane ko"

"Am sorry am sorry abun ne ya dameni, yanzu mene ne abinyi?"

Cikin Muryar kuka Tace " I don't know, I don't know am in a mess Wallahi, idan Haisam bai yafe min ba Nima bazan yafe kaina ba"

"kiyi ta istigfari Sannan muyi fatan Allah ya bashi Lafiya, kin san fa Allah ba ya yafe laifin wani wa wani"

"Ba Wannan ba, asirin Nan nake so a karya shi, don kin San Boka yace bazai tab'a daina Sona ba har ya mutu sai dai idan Mun tone abinda muka binne"

"Ta kwana gidan sauki sai muje mu cire shi"

"Shikenan hakan za'a yi zamu had'u gobe Insha Allah"

Ta Mike kana ta Tace "Ni zan tafi sai anjima Amma Banga Mama ba bata nan ne?"

"Eh sun fita da Ya Ma'aruf"

"Or Ya Ma'aruf d'in kin Nan yaki aure ki had'a ni dashi Mana"

"Tab d'i"

" Me na wani tabd'i?"

" To babu babu muje na raka ki" a zuciyar ta Kuma Tace "Allah ya sauwake mu had'a jini da ke"

Har jikin motarta ta raka ta, sai da taga fitar ta ta koma cikin gida.

Ma'isha tundaga Wannan ranar kullum a asibiti take kwana take ta wuni idan ta koma gida to dalili ne Mai karfi dake a kwai bathroom na staffs hakan yasa ta kanyi wankan a Chan Amma ta fiye yi a gida, Bayan likitocin dake kula dashi ita kadaice ake bari ta Shiga kansa Nan ma sai ta sa wani irin rigar Wanda baya Kara dama an tanadar dashine sabida Shiga ICU sannan suna da takalmi na musamman idan ta Shiga takan d'auka wa Umma hoton sa ta tura mata ko kuma in taje gidan ta nuna Mata.





Duk sanda ta Shiga gunsa idan ta fito Sai tayi kuka, ga Nan mutum amma ba Hali yayi magana.

Kwan a tashi asarar Mai Rai, wasa wasa Haisam ya kaie shekaru har biyu bai tab'a motsi ba.

Daddy,mummy da Ma'isha ne zaune a parlor, gyara  Zama Daddy yayi yace "Daughter na Kira ne don ina so muyi wata muhimmiyar magana"

"To daddy ina sauraron ka"

" Yaron Nan Ma'aruf magabatan sa sun Zo nema Masa auren ki Amma nace sai na ji ta bakin ki tukunna, kina son sa?"

Ma'isha ji tayi gabanta na duka uku uku baki na rawa Tace "Daddy aure Kuma?"

Mummy Tace "yes Mana Ma'isha so kike mu zauna mu zuba miki ido kina abinda Kika ga Dama? Isha idan ma bacci kike ki farka kina neman kusan shekaru 29 a duniya Amma har yanzu kin kasa fidda miji Kuma bawai kin rasa mane ma ba"

Cikin Muryar kuka Tace "Mummy ni gaskiya ban shirya aure yanzu ba"

Mummy Tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji ko? Yarinyar Nan so take ta jaa Mana zagi a gari shiyasa tun farko nace ba sai kaji ta bakin ta ba asa rana kawai.

Post a Comment

أحدث أقدم