DANGIN UBA
kallon Yayan ta Mardiya tayi kana ta sunkuyar da kanta kasa tace "Tun ranar da na ganki a cafeteria da Haisam na gane ki, sabida nasha ganin hotunan ki a wayan Meerah, Ayrah ta nuna min tana son sa nice na zugata mukaje gun Boka aka asirce shi, sannan ta bini akan muje mu tona naki, Haisam bazai tab'a son wata ba in har Wannan layan na kasa"
Isha Mikey tayi cikin Muryar kuka tana ambaton sunan Allah tana fad'in "Mardiya why? Mardiya me muka miki haka da kike son ganin mun wulakanta?"
Cikin Muryar kuka Tace "Kin cuce ni kin cuci masoyina bazan tab'a yafe miki, a dalilin Kune na kamu da ciwon zuciya, sannan a dalilin kune Yayana Yana chan yana kwance Rai a hannun Allah, bazan tab'a yafe muku ba"
Durkusawa mardiya tayi ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko Tace "Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min, wallahi alhakin kune yake ta bina gashi na gama makaranta sama da 3 years Amma babu Wanda ya tab'a zuwa gidan mu da sunan yana Sona, in ko an min zancen Soyayya to jikina suke so Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min"
Meerah itama mikewa tayi a tsawace Tace "yafiya? Har kina da bakin neman yafiya a wurin mu? Shin zakiyi iya Dawo min da budurcina da kimata da na rasa a dalilin ki?" Isha ta d'aura da fad'in "Shin Zaki iya Dawo min da Yayana? Zaki iya sa ya tashi? Ko Kuma zaki iya bani lafiya" Cikin tuhuma suke mata maganar.
Meerah Tace "Baza ki iya bako? To kamar yadda baza ki iya Dawo da wa'an nan abubuwan da muka rasa a dalilin ki ba Haka baza mu iya yafe miki ba" riko hannun Isha tayi da niyar barin d'akin har sun Isa kofar fita, Ma'aruf yace "Isha please " a hankali suka juyo suna kallon sa, ya karasa inda suke yana matsar kwalla yace "Nasan an zalin ce ku, har abada abinda kuka rasa baza su Dawo ba, Dan Allah ina rokon ku, ku yafe mata on my behalf, and please Isha Kar abinda Kanwata ta aikata a gare ki ya sa ki janye maganar aurena dake"
Murmushin gefen baki tayi kana Tace "It can never happened"
Cikin rashin fahimta a d'an kid'ime yace "What? Isha please Kar kice baza ki aure ni ba Dan Allah"
A d'an razane ta d'ago kanta had'e da mikewa jikin ta na kyarma cikin rawar murya Tace "Na. Na'am Yaya"
Cike da takaici ciza leb'en sa yayi yace "Are you happy now? Kinji dad'i ko? A dalilin ki na rasa masoyiyata"
"Wallahi yaya ban sani ba, ban San itace wacce kake so ka aure ba da ban....... "
A tsawce ya katse yace "Da bakiyi me ba? Oh sai kin San cewar zan aure ta ne tukkunna kisan abinda ya kamata? Who gave you the right to mingle in someone's life? Me suka miki? Nace me suka Miki?" Ya karasa maganar cikin tsawa har Saida ta razana ta jaa da baya a tsorace cikin Muryar kuka Tace "Yaya please" daka mata tsawa yayi ya nuna ta da 'dan yasa yace "This will be the last day da zaki sake kirana da wannan sunan Ni ba Yayan ki bane, daga yanzu na yanke ki daga jikina" ya Kama hanyar fita da gudu ta karasa inda yake ta rike kafafun sa tana kuka had'e da bashi hakuri, hankad'e ta yayi da kafar sa ta buge bakin ta a Kan tiles d'in dake gun Nan da nan bakinta ya Kumbura ganin ya fice ta bi Bayan sa cikin sauri.
Wurin motar sa ya nufa ya shige ganin tasa hannu ta bud'e motar zata Shiga a tsawace yace "Kul Kar ki soma Wallahi Kika kuskura Kika Shiga min mota sai na karya ki kinji na gaya miki" marfin motar ta rike ta sandare tana kallon sa tsaki yayi ya sa hannu ya ja marfin motar sa da karfin gaske ya rufe ya had'a da yatsanta , wani Kara ta saka har da ya tsorata, da sauri ya fice daga motan, hannun ta ya cire ya na mata sannu had'e da hura mata hannun (Nace Allah sarki jini kennan duk da yana fushi da ita amma ya damu da lafiyar ta) yana tuna abinda tayi ya ture ta had'e da rufe marfin motar sa ya zaga ya shige ya sa wa motar key Mai gadi ya wangale Masa gate,Mai gadi yana masa sannu da fitowa Amma bai kalle sa ba bare ya amsa,ficewar sa kawai yayi.
Mai gadi girgiza kai yayi had'e da fad'in "Anya Lafiya kuwa?"
Sai ya hango Mardiya a tsaye tana kuka ta rike hannu ta tana kallon raunin da Yayan ta ya ji mata, da sauri ya karasa inda take yana mata sannu ganin jinin da yake zuba a hannun ta, yana mata magana bata kulashi, hanyar fita tayi Yana kallon ta har ta fice, tab'e baki yayi had'e da fad'in "Tooooh Allah shi kyauta."
"Ina fa Lafiya ina ka baro min yarinya, Kun fita tare Kuma ka Dawo kai kadai"
Shiru yayi a zuciyar Kuma yace "Kash Ma'aruf ka kwafsa kasan Dole sai an tambaye ka inda take" a karo na biyi ta Kuma cewa "Ina magana kayi Shiru Ina take?"
Yes" Muryar ta ya jiyo a ta Bayan sa tana fad'in "Gani Nan Mama"
"mtsww dama kuna tare Kuma shine ina tambayar ka kayir Min shiru"
Shiru yayi baice mata komai ba, mardiya inda Mama take ta nufa ta zauna a gefen ta, idon Mama ne ya sauka a hannun ta da yayi jajir jini yana d'an sauka a hankali cikin tashin hankali Tace "Subhannallah Auta me ya same ki?"
"Mama na....."
Charafff ma'aruf ya kase ta da fad'in "Wurin rashin hankalin ta man, ta datse hannun ta a marfin mota"
Hannun ta rike tana mata sannu Tace "Amma shine Kuka Dawo gida baka kaita asibiti ba? Haryanzu fa jini yana zuba"
Yace "itace fa, Babu yanda banyi da ita ba muje Taki wai in muka dawo gida zata sha magani shiyasa na kyale ta"
Mardiya kallon sa tayi cike da mamakin karyar da yake,ganin tana kallon sane hakan yasa ya mata wani irin muguwar Kallo,da sauri ta kawar da kanta.
"idan ita bata da hankali kaima baka dashi Kenan? Maza ka d'auke ta kuje asibiti"
Ba don yaso ba ta fita tabi Bayan sa, ta tarar ya Shiga mota har ya tada ta, ta bud'e gidan baya zata zauna a tsawace yace "Ni d'in driver kine da Zaki zauna a baya don gidan ku?"
"a gaskiya Isha wannan shawarar da Kika yanke bata yi min ba Sam" Meerah kewa Isha Wannan maganar.
Isha kallon ta tayi da kamar baza ta tanka mata ba sai Kuma tace "Koh?"
Meerah ta amsa da "Kwaraai ma kuwa"
"To ni yamin"
"Yes Isha Kenan, ya kamata ki gane wani abu Mardiya daban haka ma Ma'aruf daban, so please kar laifin wani ya shafi wani please"
"Dole ya shafe shi sabida kanwarsa ce, Akan me zan zauna da irin Wannan mutanen sai su kashe ni ai"
"Babu Wanda zai kashe ki Isha, sanin Kanki ne Ma'aruf mutumin kirkii ne, shikan sa baiji dad'in abinda tayi ba please ki bar maganar nan iya mu Dan Allah"
Kallon ta tayi kana ta girgiza Kai tace "Da ce miki nayi zan kai maganar wani gun?"
"To what's the difference Tunda Kince kin fasa auren sa, idan Kika fad'awa daddy dole sai kin Sanar Masa da dalili Kinga Kenan bak tsaya a iya Nan ba"
"Uhmn Wai yaushe nace miki bazan aure shi ba? Kawai dai naji kamar na fasa ne"
"To Dan Allah Kar ki ji kin fasa,Wallahi mutumin kirkine Kuma yana sonki"
"To naji,ke dama ai bakya son laifin sa"
"A'a gaskiya dai na ke fad'a idan yayi laifi Kam Dole a hukunta shi"
"Meerah sarauniyar dad'in baki"
"No kema kin san ni ai gaskiya nake fad'a miki"
"To naji mubar zancen please kaina har wani sarawa yake"
" Dole ai ni kaina hakan nakeji"
"Allah ya kyauta ya mana Mai kyau"
Meerah ta amsa da "Ameen"
Nan sukayi ta hirar su har Saida akayi sallar Isha ta tafi.
Mummy kuwa bata tafi ba har Saida daddy ya taso daga gun aiki yazo ya d'auke ta suka wuce gida.
Washe Gari
"Auta je ki dubo yayin ki har karfe 9 bai fito ba ko Lafiya"
Jin an ambaci sunan sa sai da taji gaban ta yayi mugun fad'iwa , Mama ganin bata Mike ta a d'an tsawace Tace "Ke Lafiyan ki kuwa? Tunanin me kike haka?"
Zumbur ta mike had'e da fad'in "Babu" tayi saurin barin gun, d'akinsa ta nufa, kirjin ta na duka uku uku ta kwankwasa kofar had'e da sallama, jin bai amsa ba ta tura kofan a hankali ta shiga, hangoshi tayi a kwance yana danna wayar sa har ta Isa kansa bai sani ba, zagayawa tayi don ganin abinda yake, hoton Isha ta gani yake kallo Duk ya manta kansa , gyara Murya tayi a razane ya d'ago kai ya kalle ta, a tsawace yace "Ke Wace irin dakikiyace da zaki shigo min d'aki ba sallama?"
Cikin sanyin murya Tace "Nayi sallama baka ji bane"
"Oh na Zama makaryaci kenan ko?"
Ka ta d'aga Masa alamun a'a. Yace "Uban me ma ya kawo ki d'akina"
"Mama ce tace Nazo na Kira ka karya"
"Naji fice min daga d'aki"
Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri nasan ban kyauta ba ,Dan Allah ka rufa min asiri Kar ka fad'awa su Mama"
"mtsww Ce miki akayi ban San me nake ba? Dole ma na gaya musu jira nake Baba ya Dawo na Sanar Masa komai da komai ya kamata su San shaid'aniyar da suka Haifa"
Durkusawa tayi tana kuka Tace "Dan Allah Yaya Kar kamin haka Wallahi zasu tsane ni"
" Mtsww Wannan Kuma ke ta shafa, indai na rasa Ma'isha Wallahi kema sai kin rasa farin cikin ki, sabida Ma'isha itace farin cikina"
"Inshallah baza ka rasa ta ba yaya,zanje har gidan su na bata hakuri Dan Allah Kar ka Sanar musu."
Nagode kwaraai da Addu'an ku, Allah ya bar kauna,gamo da Typhoid da malaria nayi Kun san Basu da mutunci.

إرسال تعليق