Dangin Uba (35 to 36)


Dangin Uba

 

DANGIN UBA

Har d'akin ya tura ya nemi gu ya zauna kana yace "yes na dawo maganar me kuke tattaunawa?"

"To ba komai fa"

Kallon ta yayi kana yace "Oooh really ba komai? Naji Ana maganar Isha na son wani wane ne wannan lucky guy d'in?"

Daram daram kirjin ta ya buga, Meerah Tace "Ya Haisam dama." Ma'isha katse ta tayi da fad'in "Yaya ya school d'in d'azu na ganka da Aunty na Kuna ta soyewar ku a love garden"

"oh ashe dama dagaske ked'in ce , Dama habibty Tace min ta ganki Amma na karyata ta, har ina fad'in inda kece zaki min magana, Ashe yaudaran kaina nayi" idon sa ya Kai kan gado ya hango BP apparatus kallon abun yake da mamaki.




Murmushi tayi Tace "Ba Haka bane dama" Katse ta yayi da fad'in "Princess ya naga BP apparatus baki da lafiyane?" Ganin baza ta amsa ba yamaida kallon sa ga Meerah da take aikin kallon sa yace "Likita me ya sami princess d'in?"

"Yaya jinin ta ne ya d'an hau Amma insha Allah zai sauka na bata magani ta Sha"

"jinin ta ya hau how comes?"

" Ga ta Nan ask her"

Murmushi tayi ta Fara inda inda yace "Tell me princess me ke damin ki? Na lura a Yan kwanakin Nan Akwai abinda ke damin ki Amma kina 'boyewa mene ne?"

"Yes Yaya kasan Exam ya sako kai to yawan tunanin exam ne da rashin samun hutu yasa"

"Oh Hakane please ki rika samun hutu sosai, kar ki wahala karatun Kuma exam yazo ki kasa Exam , Kinga anyi ba'a yi ba Kenan"

"Hakane Insha Allah zan kiyayye"

Mikewa ya musu sallama ya fice. Sai da Meerah tayi sallar Isha , Ma'isha ta maida ta har gida da kanta.

Haisam ne a d'akin Umma cikin sanyin Murya da kamar rarrashi yace "Umma please, Dan Allah ki duba lamarin nan"

"Haisam Kenan, haryanzu baka fahimce ni ba Sam, bazan iya auran wani ba Bayan mahaifin ka zan cigaba da Zama haka har nima mutuwa ta riske Ni"

"Umma ki dubi girman Allah ki sake tunani a Kai, kar ki manta fa Daddy shi ya taimaka mans muka fita daga cikin kuncin Rayuwa har muka dawo Mutane, kin San abubuwan da bazan iya lissafa su ba, yau yana neman abu a wurin Wanda zamu iya bashi Kuma mu hana shi, Idan mukayi hakan ba muyi Masa butulci ba kuwa?"

A razane ta d'ago kanta ta kalli Haisam d'in kana ta sake kawar da kanta, ba Tace Masa komai ba magana yayi tayi Yana bata hakuri Amma bata tanka Masa ba har ya gaji yayi shiru mikewa yayi da niyar fita, har yasa Kai ya tsinkayo Murya Umma tana fad'in "Shikenan Na amince"

Da d'an saurin sa ya dawo cikin d'akin ya d'an rungumeta ta kana ya sake ta yace "Yauwa Umma ta ai nasan Zaki amince" mikewa yayi Yana fad'in "zani  na fad'awa Mummy"

"Wa ya aike ka? Ka bari da kaina zan Sanar da ita dama yanzu zan Shiga part d'insu"

Murmushi yayi yace 

"Shikenan Umma"

Mikewa tayi ta d'auki mayafin ta, ta nufi part d'insu mummy ta tarar a parlor sun dad'e suna Hira sama sama kamun ta fad'a Mata cewar ta amince mummy murna yasa ta Kira daddy a waya ta Sanar mishi, yayi farin ciki sosai shima Nan take ya Sanar da Abba, Abba baiyi kasa a gwiwa ba yasa aka tura masa number ta Sannan  mummy ta bata na Abba, Ba 'bata lokaci ya neman Soyayyar ta.






Haisam kuwa d'akin Isha ya Shiga ya Sanar da ita labari Mai dad'i tayi murna sosai, Nan sukayi ta hirar su.

BAYAN WATA 5

Shirye shiryen biki su ke tayi duk da ba wani events zasuyi ba daga walima sai walima shima anan gidan su Ma'isha kawai za'ayi.

Yayin da Haisam da Aysha wata soyayya ce Mai karfi ya Shiga tsakanin su kusan kullum suna tare, Ma'isha kuwa damuwa Sai abunda ya karu, Meerah kuwa kusan ko wani sati zata Zo ta duba lafiyar ta sannnan ta bata shawarwarin da ya Dace Amma Duk da hakan Isha ta kasa daina son Haisam.

Alhamdulillah an d'aura Auren Umma da Abba sannan Amarya ta tare a gidan ta anan cikin garin gombe, Daddy ne yayi iya bakin kokarin sa ganin ya dawo da dukkanin aikin Abba a gombe.

Ma'aruf kullum cikin Kiran Meerah yake Akan maganar Ma'isha, Amma Ma'isha Taki bada had'in Kai shi Kuma ya kasa hakura.

Wannan Kenan

Aisha please think about it Mana, Wallahi ma'aruf na sonki ke ko tausayin sa bakya ji? Ki duba kiga ni fa tun d'azu Yana waje Yana jiran ki Amma kin ki, ki saurare shi"

"Nifa na Riga na fad'a muku bana son sa Kuma bazan tab'a son wani ba bayan Haisam meyasa Kika kasa fahimta na ne?"

"To ai Banga amafanin hakan ba, tunda kin kasa fad'a Masa har yayi nisa da soyayyar wata hakan zai tabbatar miki da cewar kin rasa shi Kennan har abada"

Hawaye na a idanun Ma'isha d'aya na bin d'aya, taji zafin maganar Meerah Amma Kuma tasan gaskiya ta fad'a mata sabida masu iya magana sukace shi Gaskiya d'aci gareta.






"Na Sani Meerah, nasan kin damu dani kin damu da farin cikina gami da lafiya ta Amma Dan Allah kar kiyi kokarin sani Dole sai na Kula shi"

Mikewa meerah tayi Tace "fine then Ni zan tafi dama shine ya ce na rako shi, ki sani baza ki sake gani na ba a gidan ku, sannan zan fad'awa Haisam halin da kike ciki" ta Kama hanya zata wuce Ma'isha ta Sha gaban rike hannayen ta tayi tana kuka "Please don't do this to me Meerah ke ce kad'ai kike saurarata ke ce kad'ai Kika San damuwa ta Akan me zakimin irin wannan hukuncin Kuma Kar ki manta kin min alkawarin baza ki tab'a fad'a wa kowa matsala ta ba"

Fin cike hannun ta tayi da karfi Tace "Dallah malama gafara min na wuce idan ke baki da shi to ni Ina dashi, idan baza ki bawa ma'aruf dama ba ya maye miki gurbin Haisam ba to Dole ne ki samu Haisam"

Har kasa ta durkusa ta rike kafafun ta tana Mata magiya Akan Kar ta fad'a Masa.

Meerah Sam Bata Jin dad'in ganin kukan ta Amma Dole ce tasa tayi Mata hakan, Dole ta samarwa kawarta farin ciki gudun Kar ta kamu da ciwon zuciya.

Cikin murya Kamar fad'a Tace "Wallahi tallahi sai na fad'a Masa in dai baza ki kula ma'aruf ba ai zab'i na Baki" mikewa Isha ta tayi ta share hawayen ta Tace "Shikenan na amince wallahi zan kula ma'aruf, Dan Allah kar ki fad'awa ya Haisam Dan Allah"

Murmushin samun nasara Meerah tayi kana ta sa hannu tana share Mata sauran hawayen dake fuskar ta.

Cike da kulawa Tace "Am sorry Isha, ki daina kuka Sam bana jin dad'in ganin ki a Haka ne shiyasa nabi ta wannan hanyan, yanzu ki d'auko mayafin ki muje Yana chan yana jiran mu Amma ki wanke fuskar ki tukkunna"

Ba musu tayi yanda Tace mata suka fita suka tarar dashi a cikin motar sa, jiki na rawa ya fito suka gaisa, Mai gadi tasa ya kawo musu kujera ya ajiye musu a inuwa, suka zauna daga bisani Meerah ta koma d'akin Isha tana jiran su, sai da suka gama hiran ma'aruf ya kirata ya maida ta gida, tun daga wannan ranar Isha ta fara kula ma'aruf lokaci zuwa lokaci Kuma Yana zuwa gidan su tun bata sake Masa har ta Fara Duk da ba son shi take ba, ma'aruf mutum ne mai abin dariya yakan sa taji ta manta Duk wata damuwar da take dashi in dai suna tare.

AFTER 1 YEAR

Sosai Ma'isha ke mayar da hankalin ta Akan karatun ta, Sannan Duk weekend a gidan Umma take yi, Haisam kuwa tunda Umma tayi aure aka rufe part d'insu ya dawo part d'insu mummy Yana d'akin sa kusa da na Ma'isha , idan suna gida sukan zauna a parlor suyi Hira Duk sanda ya kawo maganar Aysha kuwa sai tayi yanda tayi ta kawar da maganar.






Ma'isha ne zaune da Ma'aruf a garden suna hirar su, labari yake Bata dariya take Sha sosai yayin da shi Kuma sai aikin kallonta yake.

Haisam kuwa dawowar sa Kenan daga gun Aysha tunda ya Shigo gidan yake kallon su, ji yayi ransa ya 'baci Amma bai San dalilin hakan ba, ya d'auki kusan mintuna biyar Yana kallon su su kuwa Basu ma ji shigowar sa ba, kasantuwar motan da tint yasa Basu ganshi ba, ajiyar zuciya yayi Sannan ya fice daga cikin motar har ya wuce Ma'isha Tace "Yaya ka dawo?"

Kirkirerren Murmushi yayi Sannan ya dawo mikawa ma'aruf hannu yayi suka gaisa turo baki Isha tayi Tace "Dama Yaya wuce wa zakayi Kamar baka ganmu ba?"

"Am sorry princess , kin San hankali shine gani ban lura bane" kallon Ma'aruf yayi Wanda shima kallon sa yake yi, da sauri ma'aruf d'auke Kan sa gani yayi ya Masa kwarjini, maganar su sukayi tayi kana ya shige cikin gida.

Ma'aruf kuwa natsuwar sa ya rasa yace "Wannan fa Yayan kine?"

"Yes Yayana Ne"

"Amma ya kuke dashi?"

"My cousin, meyasa kake tambaya?"

"No Bakomai naga Kuna Kama ne shiyasa"

Murmushi kawai tayi gani kawai tayi ya mike yace zai tafi, ba don taso ba ta rakashi jikin motar sa, sai da taga fitan sa ta koma cikin gida.






Kamar wasa Ma'isha tana final year kasantuwar pharmacy 5 years akeyi shi Kuma Haisam saura Masa shekara d'aya ya gama, Meerah kuwa ta dad'e da gamawa har tana aikin ta a medical center dake cikin garin gombe.

Bayan Ma'isha tayi graduating Abba ya sa ma mata aiki itama a medical center hakan yasa kullum suna tare da Meerah, Haisam kuwa kullum cikin bibiyar Aysha yake da ta gabatar dashi gun iyayen ta Amma taki kullum amsar d'aya take bashi zan had'a ku idan lokaci yayi.

Yau ma hakan Tace Masa "haba Habiby saurin me kake Ne Kam"

"Aisha!!!

Jikin ta ne yayi sanyi da jin yanda ya Kira sunanta ta amsa da "Na'am" tashi  yayi ya zauna daga kwanciyar da yake wayan dake hannun sa ya maida d'ayan kunnen nasa yace "Anya kina Sona kuwa?"

"Wannan wace irin tambaya ce Haka, kafi ko wa Sanin irin soyayyar da nake maka Kuma kake min irin Wannan tambayar?"

"I doubt much gaskiya in dai dagaske kina sona ki barni na tura su Daddy gidan ku gudun Kar wani ya shige min"

"Allah kar ka damu habiby next year fa zaka gama karatun ka kaga Ni Kuma sai Nan da 2 years na maka izini kana gamawa kazo ko da kuwa baka Sanar dani ba in yaso sai na gama a gidana ko"

Dad'in maganar natan yaji Amma ya basar yace "Shikenan sai anjima zan Zo gidan"

Da sauri Tace "A a kar kazo"

Cike da mamaki yace "Meyasa?"

"Yes Dama, Dama Mom ce ta aike Ni zanje gidan kanwarta sai dai idan zamu had'u a Chan"

"Okay wani unguwa ne?"

"Federal low cost"

"Or unguwar mu nema idan kin Zo let me know"

Bai jira yaji abinda zata ce ba ya kashe wayar, d'akin isha ya nufa ya tura kofar yaga wayam Bata nan.

Layin ta ya Kira tana picking yace "Yau weekend ina Kika shi ne, tun safe ban ganki ba?"

"Wallahi Yaya ina gidan Umma ne"

"Shine baza ki fad'a min ba mu je tare?"

"Am sorry na Shiga d'azu na ga kana baccine shiyasa"

"okay Nima gani Nan zuwa"

Ta amsa da "okay" sai ta kashe.

Haisam dama da already yayi wanka Kaya kawai yasa ta fice, ya nufi gidan mummy, sai Bayan da iya sane ya tuna ya bar wayan sa a d'akin, ganin yanda Umman sa tayi kyau tayi fresh hakan yasa shi jin dad'i sosai.






Umma na zaune a kasa, gata da babban ciki Wanda haihuwa yau ko gobe, Isha ganin tana wahala sosai ta fad'awa mummy zata zauna anan har sai Umma ta haihu Kuma ita kad'ai take aikin ta ga ciki, ita Ma'isha kullum mamaki take meyasa su Daddy basa son Yar aiki a gida.

Aysha kuwa ta Kira layin Haisam yafi sau a irga har ta koma gida bai kirata ba , a ranar Kam raba dare yayi Yana rarrashin ta dakyar ya Samu ta hakura.

Ma'aruf kuwa Duk sanda yake son ganin Isha Yana zuwa asibiti su gaisa sama sama yayi tafiyar sa ganin ta koma gidan su Umma yasa ya Fara zuwa gidan nasu, shi Sam bai San dalilin da yasa baya son ganin Haisam ba, Kuma hankalin sa ya kasa kwanciya shi duk tunanin sa Soyayya suke, sai da Meerah ta tabbatar Masa da cewar shakuwa ce kawai irin ba Yan uwa da Yan uwa.

Wata Rana, cikin dare Isha taji Umma na Kiran sunan ta , da gudu ta fita ganin Umma a cikin jini yasa tayi matukar tsorata gashi Abba baya gari Sannan Kuma karb'an haihuwa ba 'bagaren ta bane, da gudu ta d'auko wayan ta ta Kira Haisam, kasantuwar unguwa d'aya suke bai Kai mintuna goma ba ya Isa da taimakon Sa da Isha suka sa ta a mota, suna Isa asibitin aka tabbatar musu da nakuda ce.

Post a Comment

أحدث أقدم