DANGIN UBA
Da Ma'isha na zaune a reception, Haisam Kam kwata kwata ya kasa nutsuwa ya zauna ya tashi ya fara kaiwa Yana kawo wa, ya dawo ya zauna.
Ma'isha tausayin sa ya kamata sai ta tuno lokacin da Umma bata da lafiya, cike da kulawa Tace "Yaya please ka zauna Mana addu'ar mu take bukata a yanzu"
"Princess wallahi na tsoratane sosai, mata suna wahala sosai wallahi duk Wanda yace zai tozarta mace ko ya wulakanta ta bai san ciwon kansa bane bare Kuma ace uwa"
"Yes hakane Kam Amma fa ga Wanda ya sani, sabida wani abun idan kaji sai kaji Kamar Duniyar Nan an Tara zallan mahaukatane, kwanaki naji labarin wani ya Mari mahaifiyar sa akan kawai Tace Masa ya aske gashin Kan sa"
"kin gani ko to wannan ina zaiga dai dai fisabilillahi"
"Allah dai ya rabamu da iyayen mu Lafiya"
Ya amsa da "Ameen summa ameen"
Tace "Amma Yaya ka fad'a wa mummy zaka zo kuwa?"
"A a wallahi a birkice na fito, Amma bara na Kira daddy"
"shi da baya Nan?"
"Eh gara shi d'in ya fad'a mata"
"Yes"
Bayan ta Isa asibitin na had'a su duka tayi ta masifa Banda hakuri Babu abinda suka ce mata, haka Umma ta kwana ba ta haihu ba sai uban wahalar da take Sha, har gari ya waye sai abin ya tashi ya sake kwanciya.
Ganin har karfe 8 tayie bata Haihuwa ba Umma Tace su koma guda Ma'isha ta had'o musu breakfast ta kawo, a gidan Umma Haisam ya ajiye ta ya Koma gida yayi wanka ya dawo gidan Umman sai da ya karya Ma'isha ma tayi wanka suka koma asibitin.
Abba na Abuja ji yake kamar ya dawo Amma ba hali kasantuwar washe gari yana da meeting da zasuyi, Daddy Kuma yana bauchi yaje yin wasu harkokin sa a Chan, anan asibiti sukayi sallar azahar, Haisam banda matsar kwalla ba abinda yake yi Mummy da Isha Kuma sai aikin rarrashin sa suke suna kwantar Masa da hankali Likita ce ta fiti fuskanta d'auke yake da Murmushi gunsu ta nufa Tace "Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya, ta Samu Twins duka Mata"
A tare su Umma suka Shiga hamdallah, Likita kuwa Tace "Amma ta zubar da jini sosai Gaskiya tana bukatar jini"
Haisam a rud'e yace "To a d'i a nawa mana"
Hannu ta d'aga Masa had'e da fad'in "Come with me." Yabi bayanta.
Sai da aka gyara su tsaf da jariran ta Mummy da isha suka Shiga suka gansu Yara kyawa Masha Allah, wayar Ma'isha ce Fara ringing picking tayi ta dafa Kai "Tace am sorry wallahi yanzu haka ina specialist ne mom d'ina ce take labour, Amma gani Nan zauwa yanzu"
Mikewa tayi Tace "Mummy zan tafi ni na manta ma yau afternoon nake karfe biyu ya kamata na karb'e ta gashi har quarter to 3 yanzu"
"Yi maza kije Allah ya tsare"
Ta amsa da "Ameen Mummy" sai da ta d'auki hoton jariran kana ta fice, napep ta Tara ta koma gidan Umma ta d'auko lab coat d'inta kana ta d'auki motar ta ta wuce asibiti, tana Isa wacce zata karb'e ta, ta tafi, wayar ta ta zaro ta turawa Daddy da Abba hotunan, Abba na gani ya kirata Yace "Dama ta haihu ne babu Wanda ya fad'a min"
"Yes Abba d'azun Nan ta haihu"
"Amma shine baku fad'a min ba tun d'azu hankali na a tashe yake"
"Yi hakuri abba wallahi Mun shafa'a ne, Kuma ance tana bukatar Karin jini"
"Subhannallahi an samu an Sa Mata?"
" Ban sani ba wallahi nima yanzu ina bakin aikine"
"okay bari na Kira su naji"
Ya katse wayar Murmushi tayi Tace "Lalllai Abba bai ma damu da yaran ba matar sa kawai ya sani" Nan ta cigaba da aikin ta.
Mummy kanta ne ya kulle ta rasa yadda zatayi , Ma'isha na gun aiki gashi suna bukatar abinci yau ga ranar Yar aiki, Kiran abba tayi ta rarrashi shi cikin ikon Allah ya amince dama akwai wacce take son Fara aikin a gidan mummy Amma ya Hana, Mummy ba tayi kasa a gwiwa ba ta kirata, ta fad'a mata Duk abinda zatayi tana zuwa Mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga sabida mummy ta Riga ta fad'a Masa hakan yasa bai tsaya tambayar ta ba.
Duk abubuwan da Mummy ta fad'awa Sadiya duk tayi su kasantuwar ita d'in Mai nutsuwa ce, Bayan ta gama ne ta Kira Hajiya ta Sanar mata akan ta gama, Mai gadi mummy ta Kira tasa ya kawo ta asibitin ta kawo musu abinci da duk da duk wani abun da zasu bukata.
Kwanakin su uku a asibitin aka sallame su, a ranar Kuma Abba ya dawo, bakin Nan a wage an kasa rufe shi, Mummy Kam gaba ki d'aya ta dawo gidan Umma tana kula da ita, bayan Nan mummy tasa Dole sai da aka samawa Umma ita ma Yar aiki, sai Bayan suna Mummy ta koma gida kasantuwar Daddy zai dawo, Twins kuwa Ana Kiran su da Aaima da Aymana.
Sosai suke samun kulawa a gun familyn gaba ki d'aya kun San Twins da Shiga Rai musamman ma ace identical Twins ne.
Haisam ne zaune shi daddy suna Kallo a parlor sai yayi Kamar zaiyi magana sai Kuma ya kasa, mummy Ce ta fito hannun ta rike take da Plate fruits ne a ciki ta ajiye a gaban Daddy, Kallon Haisam tayi Wanda ya Shiga duniyar tunani, Kiran sunan sa da tayi "Son!!! Ne ya dawo da shi daga tunanin da ya Lula ya amsa da "Na'am Mummy"
"Lafiyan ka kuwa?"
"Lafiya Lau Mummy"
Murmushi daddy yayi yace
"Tun d'azu na lura dashi Akwai abinda yake damun sa amma yayi shiru, ka fad'a Mana Son me ke faruwane? Ko dai matsalar daga gun aikine?"
"A a daddy dama" Sai Kuna yayi shiru yana Sosa keya daddy yace "Feel free man, ka Fad'i Duk abinda kake so ni Kuma na maka alkawari zan maka shi in bai fi karfina ba"
"Umm dama. Dama Akwai wacce Muke soyyaya da itane , to ina so a nema min auren tane"
Murmushi mummy tayi Haka shima daddyn yace "Wace ce Kuma Yar gidan wace ce?"
"Sunanta Aysha,Amma Gaskiya daddy tun da muke ban samu damar ganin mahaifin ta ba, Amma na San gidan su"
"Toh Shikenan ba matsala, sai ka Sanar da ita su sa mana Rana"
"Daddy Kuna iya zuwa gobe ma don munyi magana da ita"
"To Shikenan dama Abban Kuma yana gari kaga sai muje goben kawai"
"To Shikenan Allah ya kaimu."
Mummy tunda Haisam ya ambaci sunan wata ba sunan Ma'isha ba sai taji ba dad'i Haisam mikewa yayi ta Shige d'akin sa, mummy cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na d'auka yaran Nan soyayya suke"
Cikin rashin fahimta yace "Wasu yaran Kenan?"
"Ma'isha da Haisam Mana Gaskiya na dad'e ina burin naga an had'a su aure"
Ma'isha ce ta Shigo cikin parlor bakin ta d'auke da sallama da kayan aiki ajikin ta da alama daga asibiti take Zama tayi a Kan kujerar da yake fuskantar su Daddy a kasalan ce ta gaida su suka amsa daddy yace "Yauwa daughter kin dawo a dai dai, ki fad'awa wannan yaron da yake zuwa wurin ki ya turo magabatan sa in har da gaske yake sai a had'a Rana d'aya da na Yayan ki shima gobe zamuje mu nema Masa aure"
Zumbur ta Mike Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Aure Kuma? Yayan aure zeyi?"
Mummy cikin fad'a Tace "Ke Lafiyan ki kuwa me haka?"
Jiki a sanyaye ta d'auki Jakarta ta haura sama da gudu tana kuka, Daddy yace "Meyasa Kika yi Haka?"
"Alhaji me Kuma nayi?"
"Baki San ma me kikayi ba?"
"Umm to Alhaji maganar aure fa akayi, sai kace zancen mutuwa akayi, Kuma Alhaji ban ma San nayi hakan ba,Amma Alhaji nifa ina ganin yarinyar Nan tana son Haisam"
"Kamarya Kenan fa?"
"Baka lura da hakan ba yanzu fa maganar auren sa da kayi ne ya razanar da ita yanzu Nan tabbata kuka takeyi"
Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Maybe shakuwa ce kawai ba soyayya bace , Amma shekaru nawa sukayi suna tare a gidan Nan ai in da Soyayyar ce da mun sani ko? "
"Hakane Kam, to Allah ya tabbatar da Alhairi"
"ameen."
Kamar yadda mummy Tace Isha kuka take tun da ta shiga d'akinta take aikin kuka Haisam kuwa Yana kwance hankalin sa kwance Yana waya sa masoyoyar sa, ya sanar da ita su daddy zasu zo gobe, tayi murna sosai harda Yar tsallen ta, Tace "Yanzu bari naje na fad'awa Mom ta sanarwa da Daddy"
"Yes ki bari mu gama wayar Mana tukanna"
"Aaa wallahi za dai muyi waya anjima zanje na fad'a mata"
"Yes habibti zumud'i Kenan?"
Cikin muryar Shagwab'a Tace "Toh habib ranar da nake jira Kenan fa kaga zumud'i dole, so kar kaga laifina"
"A a Banga laifin ki ba ko kad'an ni kaina na kosa goben tayi, don a gaskiya ban so auren mu ya wuce Nan sa da 3 Months"
Zaro Ido tayi kamar yana kallon ta tace "Har 3 Months Gaskiya yamin Nisa Habib"
"A hakan yayi nisa? To ya ya kike so ayi?"
"Nan da 2 months dai,kaga dama muna Shirin Exams ne zamu samu hutu Mai d'an tsayi kawai sai ayi"
"To Shikenan hakan za'ayi zan Sanar wa su Daddy idan sun amince Shikenan"
"Zama su amince,yanzu dai bye naji kamar daddy ya Shigo"
"Bye" ta katsewayar, da kanta ta Sanar da dad halin da ake cike Murmushi yayi yace "Yaran zamani ba kunya wato ma zan yi baki Shikenan Allah ya Kai mu goben sai sun Zo"
"To Daddy."
Ma'isha kuwa sai da tayi kuka Mai isarta kana ta fito parlor mummy Tace "Dama yanzu zan Shiga na duba ki Lafiyan ki kuwa?"
"Lafiya Lau Umma"
"Ya naga idanun ki sun Kumbura?"
"Bacci nayi Mummy,an gama abinci?"
Mummy ta amsa da "yes an gama,Yau anan Zaki Kwana ba gidan su Abba ba?"
"Yes Mummy sai jibi zan koma chan d'in"
"To Shikenan Allah ya kaimu,zo muje dining d'in.
A tare suka zauna Ma'isha Tace "Mummy ina daddy?"
"Ya fita yaje gidan Abban ku zasuyi maganar zuwa gidan su budurwar Yayan ki"
Ma'isha ji tayi kamar zuciyar ta zata buga,ganin irin kallon da Mummy take Mata tana son gane wani abu tayi kirkirerren Murmushi Tace "Nifa na d'auka Yaya is not serious about her"
"Dama kinsan tane?"
"Yes na santa ita ma a school d'in mu take course d'insu d'aya da yaya"
"Kina so kice min course mate d'insa ce"
"Eh to kusan hakanne Amma fa ba aji d'aya suke ba,sune zasu Gama a shekarar Nan"
"Oh Masha Allah, Yayan naki Kinga na manta kije ki kirashi yazo yaci abinci"
Ta Mike Kenan ta hango shi Yana saukowa hannun sa a manne a kunnen sa yana waya Yana dariya,Zama tayi Tace "Gashi Nan ma"
"Okay"
Sai da ya gama wayar yazo ya ja kujera had'e da fad'in "Barka da Dare Mummy"
"Yauwa Barka son,yanzu nake ce mata ta Kira ka sai ga kanan,waya ake tayi haka da surkuwa ta?"
Murmushi yayi kawai baice mata komai ba, Ma'isha tace "Yaya ina wuni"
"Lafiya Lau princess, pharmacists of the house ya na ganki haka? Baki da lafiya ne?"
"Bacci na wuni yi Yaya"
Mummy Tace "Wai wuni naga Bayan la'asar Kika dawo"
Haisam yace "Mummy Amma baki lura kamar princess na cikin damuwa ba?"
"Gata Nan dai nima na lura da hakan Amma na tambaye ta Tace min bakomai"
Mikewa yayi yace "Bari naje naji ko mene ne."
Bai jira yaji amsar ta ba ya haura sama da sauri, tun daga kofar d'akin yaji tana ta dariya, a hankali ya tura yaga tana waya Zama yayi tana kallon sa Amma Bata kashe wayar ba,ta d'auki kusan 5 minutes Kan ta katsewayar da fad'in "Sorry Love zan Kira ka yanzu"
Haisam ji yayi wani abu ya tokaresa a wuya Ma'isha Tace "Am sorry yaya wallahi Ma'aruf ne yake ta bani dariya"
Cikin rashin Jin dad'in maganar nata yace "Waye ma'aruf?"
"Saurayina man Yaya Wanda yake zuwa gidan Nan"
"Oh that guy? Ni ban San sunan sa ba"
"Ma'aruf sunan sa"
"Ban San me Kika gani a jikin sa ba Ni Sam bai min ba"
"Yaya saurayin nawa ne bai maka ba? Aiko shi nake so Kuma zan aura"
"Yes lallai gani nake Sam baku dace ba"
Ma'isha wayanta ta bud'e ta Shiga gallery ta Mika Masa wayan had'e da fad'in "have a look"
Karb'a yayi ganin hotunan da suka d'auka tare sauran selfies ne sauran Kuma d'aukan su akayi suna dariya a wurare da dama,sauran gun wurin cin abinci ne da ice cream Rai a 'bace ya Mika mata wayan yace "ba laifi maybe ranar kallon tsoro na Masa,Kuma yana sonki?"
"Yes Mana sosai ma yana sona ga alamu Nan, hotunan Nan da ka gani ai sun Isa ka gane hakan"
"Hakan yanzu auren sa zakiyi?"
"Yes insha Allah,daddy ma yace na fad'a Masa ya turo don Yana so a had'a ayi rana d'aya"
"Me za'a had'an"
"My wedding and yours"
Mikewa yayi yace "Yayi kyau"
Ya fice Isha kuwa d'aga kafad'a tayi irin halin ko in kula d'in Nan ta Kira Ma'aruf ya katse kana ya kirata suka cigaba da wayar su.
Haisam kuwa Yana Shiga d'akin sa ya kasa tsaye ya kasa zaune ya rasa dalilin da yasa yaji duk ya damu baya son Ma'isha ta auri gayen Nan, dafe kansa yayi yace "Maybe ko don gayen baya burgeni ne?"
Ya kuma bawa kansa amsa da "Hakanne ma?
Wayar sa ya d'auka kamar zai Kira Aysha sai kuma ya fasa ya kashe wayar gaba ki d'aya ya kwanta dakyar da makyar kyasa bacci ya sace shi.
Washe Gari
Karfe hud'u na yamma,Daddy da Abba suka shirya don zuwa gidan su Aysha , Haisam ke Jan motar yayin da Abba ke gefen sa daddy Kuma yana baya suna tafiya suna Hira har suka Isa.
Haisam na ganin su Daddy yace "habibty ganan su Daddy sun fito zamuuyi waya anjima"
Cikin muryar Shagwab'a Tace "Bazan ganka ba Kenan?"
"Zan dawo anjima insha Allah, bari Muji yanda sukayi tukunna"
"Insha Allah,Mai dad'i ne sabida dad yasan ina son ka,Kuma yana son abin da nake so"
"To Masha Allah,I'll call you later." ya katse wayar.
Su dad kuwa har jikin mota suka raka su daddy hakanne ya tabbatar Masa da cewar bashi da sauran matsala,ai kuwa suna fita a gidan daddy ya Sanar Masa da and ranar bikin Nan da wata biyu, Haisam farin cikin da yake ciki ya kasa 'boyewa, gidan Abba Suka nufa Umma taji dad'i ta wani 'bangaren wani 'bangaren Kuma bata ji dad'i ba Sam,sabida kullum burinta shine Haisam ya auri Ma'isha tayi wa Abba korafi yayi saurin dakatar da ita akan ba a yi wa d'an yau auren Dole.
Shiri suka Shiga yi duka family Ma'isha ma ba'a barta a baya ba,idan tana cikin Mutane ta nuna tafi kowa farin ciki yayin da idan tana d'akin ta Kuma taci kukan ta,son ranta idan ta gama ta wanke fuskar ta.
Yau saura sati d'aya bikin Aysha da Haisam, Ma'isha da Meerah na gani zaune a cikin Masallacin asibiti da alama sun idar da sallar ne "Isha kiyi hakuri Dan Allah, Rana ita yau fa auren su,kema sai da nace miki ki tura Ma'aruf Amma kinki har karya fa kikayi wa Daddy cewar Ma'aruf baya Nan Bayan kuma yana Nan,ban San dalilin ki nayin hakan ba"
" Dalili d'aya ne kema kin sani,Haisam nake so ba Ma'aruf ba"
"Na sani amma ai Haisam d'in aure zaiyi ko?"
"Yes Ana gama auren sa zan fad'awa Ma'aruf ya fito"
"Ikon Allah,to Allah ya nuna Mana"
"yanzu Meerah ya Haisam aure zaiyi fa ko? Kuma wata zai aura bani ba?" Ta fashe da kuka Mai cin raai har Saida sauran staffs d'in suka Fara kallon su rarrashin ta Meera keyi sai da tayi mai isarta ta Mike Kenan ta yanke jiki ta fad'i sumammayi.
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe baba.

إرسال تعليق